Shuwaka da Turanci kuma Bitter leaf yarbawa suna kiran ta da Ewúro sai kuma Igbo onugbu Ityuna da yaren Tiv, oriwo Edo, Awɔnwono (Akan), harwa yau Hausawa suna kiran Shuwaka da 'chusar-doki: , mululuza da yaren Luganda, labwori da yaren Acholi, olusia da yaren Luo, ndoleh da yaren Cameroon da kuma Olubirizi da yaren Lusoga.[1] ita shuwaka wata nau'in bishiya ce ko kuma wata itaciya ce wadda take da ganye kore wanda akanyi miya da ganyen ta ɗin musamman miyan tuwo, shuwaka tana ɗan yin girma daidai gwargwado don tsayin ta yana kaiwa mita 1,200 (3,900ft) zuwa mita 2,000 (6,900ft) kenan sai kuma ganyenta yana kai tsayin mita 6-8 ganyen ta ko sabo ko tsoho duka sunada tsami/bauri, a lokacin da mutum yake cin ganyen ta zai dinga jin wannan tsami/ɗaci amma bayan ya gama zuwa wani lokaci sai ya fara jin zaƙi a cikin bakin shi da maƙogwaro ko kuma bayan ansha miyarta.[2][3]

Shuwaka
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderAsterales (en) Asterales
DangiAsteraceae (en) Asteraceae
TribeVernonieae (en) Vernonieae
GenusVernonia (en) Vernonia
jinsi Vernonia amygdalina
Delile, 1826
ƙaramin bishiya shuwaka da ganye kore shar
yanda ake sarrafa fate acikin miyan shuwaka
ganyen shuwaka

Wajen da shuwaka tafi fitowa

gyara sashe

Masana da masu Bincike sun tabbatar cewa shuwaka tafi fitowa a gefen rafi da cikin kurmi da kuma gefen hanya wato dai tafi son wajen da yake da damshi-damshi wajen da ba foƙo ba. Mutane da dama Basu san alfanun shuwaka ba sai dai masana sun bayyana wasu daga cikin amfanin da take da shi ga ɗan Adam

Amfanin shuwaka

gyara sashe

Amfanin shuwaka sunada yawa amma dai ga wasu kaɗan daga cikinsu:[4][5][6]

  • Ana tafasa shuwaka da ruwa a sha yana maganin ciyyon sigar jini (blood sugar)
  • Tana maganin ciyyon hawan jini (blood pressure)
  • Ana cin sabon ganyenta don magance ciyyon gaɓɓai da ciyyon sigar (diabetes)
  • Haka tana maganin cutar ƙiba
  • Cin gayen shuwaka sau uku a rana yana maganin kansa (Cancer) safe, rana da yamma zai ci ganye daga 5-7 a wuni
  • Tana daidai ta jiki
  • Tana ƙara kuzari yayin mu'amalar aure
  • Tana maganin ciyyon zuciya
  • Shuwaka tana maganin amai da gudawa
  • Shuwaka tana maganin tsutsar ciki
  • Shuwaka tana maganin ciyyon ƙoda[7]
  • Shuwaka na wanke dattin ciki
  • Shuwaka tana maganin zafin ciki
  • Shuwaka tana maganin basir mai sanya kumburin dubura.

Yadda take taɓa masu ƙoda

gyara sashe

Marasa lafiya musamman Masu fama da ciwon ƙoda ko hanta (kidney disease) an hana su cin shuwaka in kuma zasu ci to kada su yawaita, kamar yadda wani mai bincike ya nuna idan mai ciyyon ƙoda yayi amfani da shuwaka na tsawon sati biyu to ƙafan sa da hannayen sa zasu fara kumburi. A takaice dai idan mai fama da ciwon ƙoda zaici shuwaka to lallai ya nema shawaran likitan shi. Duk da cewa koma menene idan aka yawaita shi zai iya cutarwa.

Manazarta

gyara sashe
  1. Egedigwe CA (2010). Effect of dietary incorporation of Vernonia amygdalina and Vernonia colorata on blood lipid profile and relative organ weights in albino rats (Thesis). Department of Biochemistry, MOUAU, Nigeria.
  2. "Yadda Ake Girka Miyar Shuwaka". aminiya.dailytrust.com. 25 January 2019. Retrieved 23 November 2021.
  3. Asante, Du-Bois; et al. (2019). "Anti-inflammatory, anti-nociceptive and antipyretic activity of young and old leaves of Vernonia amygdalina". Biomedicine & Pharmacotherapy. 111: 1187–1203. doi:10.1016/j.biopha.2018.12.147. PMID 30841432.
  4. "amazing health benefits of bitter leaves". publichealth.com.ng. 28 October 2019. Retrieved 23 November 2021.
  5. Nura Bala, Abubakar (25 January 2019). "LABARAI: Cuttuka 20 da shuwaka ke warkarwa a jikin Dan Adam". legit.hausa.ng. Retrieved 23 November 2021.
  6. Muanya, Chukuma (9 May 2019). "How bitter leaf prevents kidney, liver, heart damage". The guidian.ng. Archived from the original on 23 November 2021. Retrieved 23 November 2021.
  7. Adejo, Chris (3 February 2017). "bitter leaf side effects". legit.ng. Retrieved 26 November 2021.