Mai martaba Alhaji Abbas Njidda Tafida Sarkin Muri, Jalingo, jihar Taraba, Najeriya. Shine sarki na goma sha biyu (12) a daular masarautar Muri, kuma ya hau sarautar ne a shekarar 1988 biyo bayan sauke sarki Alhaji Umaru Abba Tukur daga karagar mulki.[1][2][3][4][5]

Abbas Njidda Tafida
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Yuni, 1953 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Fillanci
Sana'a
Sana'a emir (en) Fassara da ɗan kasuwa

Haihuwa gyara sashe

An haifi mai martaba sarkin Muri Alhaji Abbas Njidda Tafida a ranar 10 ga watan shida na shekarar 1953 a cikin garin Jalingo babban birnin jihar Taraba. Alhaji Abbas ya kasance daga tsatson marigayi Lamido Nya Jatau wanda kuma ya kafa garin Jalingo kuma jika ne ga Lamido Mafindi, sarki na tara a daular.[6][7][8]

Karatu gyara sashe

Mai martaba Alhaji Abbas bayan karatun Islamiya da na Alqur'ani mai girma da yayi, ya shiga makarantar firamari na Mohammadu Nya Primary School dake garin Jalingo a shekarar 1961 har lokacin da ya kammala a shekarar 1967. Bayan kammala makarantar firamarin, mai martaba ya ci gaba da karatunshi na sakandari a Government College Keffi wanda yake a jihar Nasarawa a yau a shekarar 1967 zuwa shekarar 1973. Bayan kammala makarantar sakandari, mai martaba ya sami takardan shiga Jami'ar Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar 1973 inda yayi karatun digirin shi a fannin kasuwanci kuma ya kammala a shekarar 1977, mai martaba ya kuma yi karatun PGD a fannin tattalin arzikin a African Development Bank, Abidjan a shekarar 1981 zuwa shekara ta 1982. Har ila yau, ya kuma kara yin wani karatun na PGD a makarantar Green Beheld Smith and Co. London a shekarar 1982 zuwa shekarar 1983. [9]

Aiki gyara sashe

Mai martaba ya kasance gwarzon dan kasuwa kuma shaharren manomi kuma ma'aikacin gwamnati, a shekarar 1978 zuwa shekarar 1979 ya yi aiki da hukumar New Nigeria Development Company (NNDC), mai martaba ya kasance babban manaja (MD) na Nigeria Hotels daga shekarar 1979 har ya zuwa shekarar 1988 lokacin da aka nada shi sabon sarkin Muri. An dai nada mai martaba sabon sarki ne a ranar 12 ga watan Yulin shekarar 1988 don maye gurbin marigayi tsohon sarki Alhaji Umaru Abba Tukur. Mai martaba Alhaji Abbas dai ya kasance sarki na goma sha biyu (12) a daular Muri.[10][11]

Manazarta gyara sashe

  1. Olagunju, Lasisi (26 July 2021). "The Honest Emir Of Muri". tribuneonlineng.com. Retrieved 5 February 2022.
  2. "THE EMIR OF MURI'S ULTIMATUM". thisdaylive.com. 4 August 2021. Retrieved 5 February 2022.
  3. "Emir of Muri, Ibarapa residents, Benue and others with sleepless nights". The cable.ng. 25 July 2021. Retrieved 5 February 2022.
  4. Isah Hunkuyi, Magaji (25 July 2021). "Weed Out Criminals Among You', Emir Of Muri Tells Fulani Leaders". daily trust.com. Retrieved 5 February 2022.
  5. Yusuf, Ahmad (22 July 2021). "Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura". legit.hausa.com. Retrieved 5 February 2022.
  6. "30-day ultimatum: Fulani herdsmen visit Emir of Muri, take oath". pmnewsnigeria.com. 2 August 2021. Retrieved 8 February 2022.
  7. "Eviction Threat: Miyetti Allah vows to fish out criminal cattle herders in Taraba". premiumtimesng.com. 3 August 2021. Retrieved 8 February 2022.
  8. "Emir Rattles Security Agencies over Death Threat against Fulani Herdsmen". prnigeria.com. 25 July 2021. Retrieved 8 February 2022.
  9. https://www.voahausa.com/a/5548728.html
  10. Baballe, Hafiz (11 August 2020). "NOMA TUSHEN ARZIKI: Hirar Da Mai Martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Tafida, Kan Manoma Da Makiyaya, Kashi Na Daya". voahausa.com. Retrieved 8 February 2022.
  11. Justin, Typuusu (22 July 2021). "Why I issued 30-day ultimatum to criminal herders in Taraba forests -Emir Tafida". punch.com. Retrieved 8 February 2022.