Sarah Reng Ochekpe yar siyasa ce a Najeriya, kuma ta fito ne daga Jihar Filato. Ta kasance Ministar Albarkatun Ruwa daga (2011 zuwa 2015).

Sarah Reng Ochekpe
Rayuwa
Haihuwa 4 Oktoba 1961 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Nelson Ochekpe (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello Digiri a kimiyya : Kimiyyar siyasa
Jami'ar, Jos Master of Science (en) Fassara : public administration (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Sarah Reng Ochekpe

Kuruciya da ilimi

gyara sashe
 
Sarah Reng Ochekpe

An haife Ochekpe a ranar 4 ga watan Oktoban 1961, ga dangin Ali Reng Madugben a garin Foron, wani yanki na ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta Jihar Plateau. Ta yi digirinta na farko a Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Ahmadu Bello, sannan ta yi digiri na biyu a kan harkokin mulki daga Jami’ar Jos. Har ila yau, tana da digiri na biyu daga Kwalejin Kasuwanci na Aberdeen da Cibiyar Nazarin Aikin Jarida ta Najeriya .[1][2]

Rayuwar ta

gyara sashe
 
Sarah Reng Ochekpe

Ta kasance tana auren Farfesa Nelson Ochekpe daga ƙaramarOhukumar tukpo daga gJihar Benue. Shi farfesa ne a fannin kimiyyar harhada magunguna kuma Mataimakin Shugaban a Jami’ar Jos.[3]

Harkokin siyasa

gyara sashe

Ochekpe ta riƙe mukamai da yawa a hukumar kula da wayar da kai ta ƙasa na (Najeriya), kafin a naɗa ta minista kenan. A lokacin da take cikin gwamnati, an lura da cewa ta kara imganta atakiansamar da ruwan sha ga 'yan Najeriya zuwa kashi( 0%) sannan kuma ta kirkira gyaran hanyoyin ruwa na roba wadanda suka rage ambaliyar ruwa, sannan ta samar da hanyoyin rage rashin aikin yi, ta hanyar samar da aiki.[4][5][6]A shekara ta (2017), ita da wasu mutane biyu an zarge su da halatta kudaden haram da hada baki da ya kai fam miliyan( 450).[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Mrs Sarah Reng Ochekpe".
  2. Adingupu, Charles (December 8, 2012). "The travails of Women Ministers". Vanguard. Retrieved 2018-05-04.
  3. "University of Jos - Governing Council | University of Jos". www.unijos.edu.ng (in Turanci). Archived from the original on 2018-11-07. Retrieved 2018-11-07.
  4. Alli, Yusuf (April 5, 2015). "What becomes of Jonathan's women?". The Nation. Retrieved 2018-05-04.
  5. "Nigeria seeks dam safety training, design, studies, supervision of dam work". January 5, 2015. Archived from the original on 2019-07-02. Retrieved 2018-05-04.
  6. Abutu, Alex (June 26, 2013). "The task of regulating boreholes". Dailytrust. Retrieved 2018-05-04.[permanent dead link]
  7. "Pwanagba, Agabus (February 13, 2018). "Alleged N450m fraud: Court seizes ex-minister Ochekpe's international passport". Dailypost. Retrieved 2018-05-04.