Sani Danladi

Dan siyasar Najeriya kuma ɗan kasuwar jihar Taraba

Sani Abubakar Danladi (an haife shi 14 ga watan Fabrairu 1968) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya zama sanata mai wakiltar mazabar Taraba ta Arewa daga shekarar 2015 zuwa 2017. A baya ya taɓa riƙe muƙamin muƙaddashin gwamnan jihar Taraba daga shekarar 2014 zuwa 2015, sannan yayi mataimakin gwamnan jihar Taraba sau biyu daga 2007 zuwa 2012, da kuma daga 2014 zuwa 2015.

Sani Danladi
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 2015 - 23 ga Yuni, 2017
Anthony George Manzo - Shuaibu Isa Lau
District: Taraba North
Gwamnan jahar Taraba

2013 - 29 Mayu 2015
Garba Umar (en) Fassara - Darius Ishaku
Rayuwa
Haihuwa 1968 (55/56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

An zaɓi Danladi mataimakin gwamnan jihar Taraba a zaben gwamnan jihar Taraba a shekarar 2007. An sake zaɓen shi a 2011. An tsige shi a daga mataimakin gwamna a ranar 4 ga watan Oktoba 2012. Kotun koli ta soke tsige shi a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2014, inda aka mayar da shi mataimakin gwamna kuma muƙaddashin gwamna don ci gaba da mulkin Gwamna Danbaba Suntai wanda ya gagara cigaba da mulkin sakamakon hatsarin jirgin sama da yayi, makonni uku da tsige shi.

An zaɓe shi Sanata mai wakiltar mazaɓar Taraba ta arewa a zaben majalisar dattawan Najeriya na 2015. Kotun ƙoli ta kore shi a matsayin Sanata a ranar 23 ga watan Yuni 2017.[1]

A ranar 7 ga Agusta 2024, Danladi ya zama Memba na Hukumar Kula da Ilimi ta Ilimi.

Manazarta

gyara sashe
  1. Shibayan, Dyepkazah (23 June 2017). "Supreme court sacks Danladi, Taraba north senator". TheCable. Retrieved 17 March 2024.