Safiath
Safiath, sunanta na haihuwa shine Safia Aminami Issoufou Oumarou (an haife ta a ranar 15 watan Afrilu shekara ta 1982), mawakiya kuma marubuciyar wakokin gambarar zamani (hip-hop) ce.
Safiath | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Khartoum, 15 ga Afirilu, 1982 (42 shekaru) |
ƙasa | Nijar |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi, rapper (en) da mai rubuta waka |
Sunan mahaifi | Safiath |
Kayan kida | murya |
Anhaifi Safiath a birnin Khartoum, na kasar Sudan,[1] yar kanilar Abzinwa da Zarma ce;[2] mahaifiyar ta yar Sudan ce yayin da mahaifin ta dan Nijar ne.[3] Mahaifin ta ya fada mata cewa tana iya zama duk abinda take son zama a duniya, maimakon ta zamto mai kwalliya, sai ta tafi kasar Morocco domin ta karanta ilimin tsimi da tattali da kuma harkar banki. Lokacin zamanta a Rabat ne ta shiga kungiyar mawaka ta Salsa, inda take kada Jita; daganan ta dawo gida Nijar inda taci gaba da wakokin ta.[4] Itace shugabar kungiyar Kaidan Gaskiya.[5] Tana yin wakokin ta ne cikin harsunan Faransanci, Zarma, Hausa da Tamashek,[4] wakokinta atasari sun tafi ne kan harkokin yau da Kullum kamar dai wakokinZara Moussa; hakanan tana taba wakoki kan yancin yara.[6][5] Haka kuma tana yin wakoki domin karfafa gwuiwa ga matasa.[3] Safiath tayi aure wanda ta aura shine Phéno, kuma suna da yaro a tsakanin su.[1] Tasha wakiltar Nijar a gasar wakoki ta kasa da kasa,[5] wanda ya hada da gasar 2013 Jeux de la Francophonie a birnin Nice,[1] hakanan ta tabayin kira ga yan kasar ta dangane da su rinka sairaren wakokin cikin gida, tace Salomon rap na Nijar nada muhimmanci fiye da wakokin Faransa da na Amurika.[3] Lokacin tashen ta, yai hadaka da mawakan wajen Nijar cikin kasashen Afrika.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "7ème Jeux de la Francophonie à Nice (France) : Le Niger sera représenté en chant par Safiath". www.lesahel.org. Archived from the original on 7 November 2017. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ "Amman Imman - Dining for Women". diningforwomen.org. Archived from the original on 1 March 2019. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Safiath, une artiste engagée". jeunesseduniger.blogspot.com. 30 March 2013. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ 4.0 4.1 "Safiath: Tazedar". abagond.wordpress.com. 29 October 2017. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "More Than We Know: Discovering Nigerien Culture Through Art". wellsbringhope.org. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ "Four Nigerien Women Musicians You Should Know". Africa Is a Country. 11 December 2013. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ "Zim in regional collaborations - NewsDay Zimbabwe". Newsday.co.zw. 27 April 2013. Retrieved 5 November 2017.