Zara Moussa
Zara Moussa (an haife ta a shekarar alif dari tara da tamanin miladiyya 1980) mawakiyar salon gambarar zamani ce yar kasar Nijar wadda akafi saninta da ZM.
Zara Moussa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Niamey, 1980 (43/44 shekaru) |
ƙasa | Nijar |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi da rapper (en) |
Sunan mahaifi | Zara Moussa |
Kayan kida | murya |
Rayuwarta
gyara sasheHaifaffiyar birnin Niamey, Moussa ta fara tashe ne a shekarar 2002 lokacin da taci kyautar hip-hop contest a birnin na haihuwar ta.[1] kyautar da ofishin jaladancin Faransa ya dauki nauyi.[2] Zara itace sananniyar mace mawakiyar gambarar zamani (wato Hip Hop) a Yammacin Afrika gabadaya da ta fara fitar da kundi (album) wanda tasakama suna Kirari. Wakokinta sunfi dangantuwa ne akan harkokin yau da kullum, siyasa da kare hakkin mata,[1] da kima harkokin lafiya. Salon Zara na kama da salon mawakiyar Nijar dinnan Safiath [3]. Yawancin wakokin ta cikin harshen Faransanci tayi su, amma akwai wadanda tayi su cikin harsunan Hausa da Zarma.[4] Salon ta yazo da wani sabon babi tsakanin mawakan hip-hop na nahiyar Afrika.[5] Moussa tayi aure, kuma ta baiyana maigidanta wanda shike rubuta akasarin wakokinta da babban jarumi kuma mataimakinta wajen habbaka harkokin wakokin ta. Musamman ma a kasar da ake kallon waka da aibi, kuma ma kasar da maza ne kadai suka mamaye harkokin wakokin na Hip Hop.[2]
Wakokin ta
gyara sasheWaka | Mintoci |
---|---|
Tout Va De Travers | 3:54 |
Ma Rage | 3:03 |
Kirari | 3:29 |
Soyeya | 3:26 |
Femme Object | 3:45 |
Femme rurale | 3:45 |
Ma Gate | 3:17 |
Violence | 4:18 |
Rapo | 3:49 |
Prends Le Mic | 3:28 |
Je Dois Patir |
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Alison Behnke (15 December 2007). Niger in Pictures. Twenty-First Century Books. pp. 70–. ISBN 978-0-8225-7147-6.
- ↑ 2.0 2.1 "Verdensmusikbanken - Verdensmusik i undervisningen - Interview med Zara Moussa". www.verdensmusikbanken.dk. Archived from the original on 4 March 2017. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ Burgess, Sarah (11 December 2013). "Four Nigerien Women Musicians You Should Know: ZM (Zara Moussa)". Africa is a Country. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ "Zara Moussa | Studio le Rocher". Studiolerocher.fr. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ "Zara Moussa - virtualWOMEX". www.womex.com. Retrieved 5 November 2017.
- ↑ https://www.discogs.com/Zara-Moussa-Zara-Moussa/release/14496272