Ouma Laouali (Sassaitar Hausa: Umma Lauwali) matukiyar jirgin sama ce, kuma mace ta farko da ta tuka jirgin sama a Jamhuriyar Nijar.

Ouma Laouali
Rayuwa
Haihuwa 1987 (36/37 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Matukin jirgin sama da soja
Ouma Laouali a Oktoba 2015.

A shekarar 2015, Laftanar Laouali, yar shekaru 28, tazama mace matukiyar jirgin sama kuma ta farko a Nijar.[1][2][3][4]

Laouali na daya daga cikin jami'ai a Rundunar Sojan sama ta Nijar da suka samu horo a kasar Amurika domin su taimaka wajen yaki da Boko Haram (kungiyar yan ta'adda a Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.[1][2] Tana tuka jirgi Cessna, biyu daga wanda Amurika ta bama Nijar a wani biki a babban birnin kasar Niamey, a wani bangare na tallafin dalar Amurika miliyan $24 na horo da jiragen yaki.[2] Zuwa Oktoba, 201 5 akwai rundunar soja ta Amurika a birnin Niamey kuma akwai rahoton za'a kara bude wani a Agadez birni a yankin Sahara ta Nijar domin yaki da yan ta'adda.[4]

A ta cewar kamfanin Ventures Africa yace mata matuka jirgin kasa na fuskantar matsalar wariyar jinsi a Afrika."[1] Laouali tashiga jerin su a jadawalin da kamfanin ya gudanar na matan Afrika na kwarai a 2015.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Meet Niger's first female pilot - Ventures Africa". venturesafrica.com. 24 October 2015. Retrieved 9 November 2017.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Ouma Laouali: Niger gets first female airforce pilot". thisisafrica.me. 28 October 2015. Archived from the original on 4 January 2018. Retrieved 9 November 2017.
  3. "Flying High! Here are the Trailblazing Female Pilots From Africa". styleyetu.com. 1 September 2016. Archived from the original on 10 November 2017. Retrieved 9 November 2017.
  4. 4.0 4.1 "Africa highlights: Thursday 22 October 2015". bbc.co.uk. Retrieved 9 November 2017.
  5. "Which African women powered change in 2015? - TRUE Africa". trueafrica.co. Retrieved 9 November 2017.