Otaru Salihu Ohize
Otaru Salihu Ohize (5 Fabrairu 1953 - 30 Oktoba 2016) ɗan siyasan Kasar Najeriya ne. Ya taba zama Sanata mai wakiltar
Otaru Salihu Ohize | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 6 ga Yuni, 2011 ← Nurudeen Abatemi Usman District: Kogi Central
29 Mayu 2007 - 2011 ← Nurudeen Abatemi Usman District: Kogi Central | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Jahar Kogi, 5 ga Faburairu, 1953 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Mutuwa | Abuja, 30 Oktoba 2016 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar jahar Lagos Jami'ar Ahmadu Bello | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Action Congress of Nigeria |
Kogi ta tsakiya a jihar Kogi daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2011. Ya kasance memba na Action Congress (AC).
Ohize ya sami digiri na farko B.Sc. Ya karanta kimiyyar siyasa a Jami'ar Legas a shekarar (1987) sannan ya yi Master of International Affairs & Diplomacy a Ahmadu Bello University, Zaria a shekarar (2003). Ya yi shekara goma sha biyar (15) a aikin sojan Najeriya da na ruwa na Najeriya [1]. Ya kasance shugaban ƙaramar hukumar Okene a jihar Kogi a karo na biyu. Bayan ya hau kan kujerar majalisar dattawa a watan Yuni shekara ta 2007 an nada shi kwamitocin wasanni, harkokin ‘yan sanda, harkokin cikin gida, yaɗa labarai da yada labarai, gidaje, kasuwanci da noma. [2] A wani nazari na tsakiyar wa’adi na ‘yan majalisar dattawa a watan Mayu shekara ta 2009, Thisday ya lura cewa bai dauki nauyin wani kudiri ba. Ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja a ranar 30 ga watan Oktoba shekarar 2016. #