Olayide Owolabi Adelami (an haife shi a ranar 3 ga watan Afrilu 1958) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Ondo tun a ranar 1 ga watan Fabrairu 2024.[1][2] Ya taɓa zama mataimakin magatakarda na Majalisar Dokoki ta ƙasa.

Olayide Adelami
Deputy Governor of Ondo State (en) Fassara

ga Faburairu, 2024 -
Rayuwa
Haihuwa Ondo
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Ibadan
Jami'ar jahar Lagos
Jami'ar Olabisi Onabanjo
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da accountant (en) Fassara
Wurin aiki Jahar Ondo
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Adelami a Owo, Jihar Ondo, Najeriya. Ya yi karatun firamare a St. Francis Catholic Primary School, sannan ya ci gaba a Kwalejin Imade da ke Owo. Ya sami takardar shaidar matakin GCE A daga The Polytechnic, Ibadan. Adelami ya samu digirin sa na BSc a fannin harkokin kasuwanci a jami'ar Legas, inda ya yi digirinsa ( Masters) a irin wannan kwas a jami'ar jihar Ogun, sannan ya yi digirin digirgir a fannin tsaro da dabarun bincike daga jami'ar jihar Nasarawa.[3]

Adelami ya yi aiki a matsayin akawu a watan Disamba 1983, a Hukumar Ma'aikata ta Tarayya. Daga shekarun 1996 zuwa 2000, an naɗa shi a manyan ofisoshi ciki har da babban asibitin ƙasa, Abuja. [3] [4]

Adelami ya zama shugaban sashin kuɗi da asusu na majalisar tarayya a jihar Ondo har zuwa shekarar 2007, inda aka naɗa shi darakta. Ya yi babban kwas na gudanarwa daidai kwas na 54 a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun Ƙasa a shekarar 2008. A shekarar 2014, Adelami ya samu muƙamin babban sakatare na hukumar saye da sayarwa, gidaje da ayyuka, rawar da ya taka har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin mataimakin magatakarda na majalisar dokoki ta ƙasa (Nigeria).[5][6]

Adelami ya fara aikin siyasa na cikakken lokaci a shekarar 2018, a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress. Gwamna Lucky Aiyedatiwa ne ya naɗa shi mataimakin gwamnan jihar Ondo a ranar 24 ga watan Janairun 2024, sannan kuma ya rantsar da shi a ranar 1 ga watan Fabrairu 2024. [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Ojomo, Olufemi. "Olaide Adelami Sworn In As Ondo Deputy Governor". Channels TV. Retrieved 31 May 2024.
  2. Tope, Fayehun (1 February 2024). "Adelami Sworn In As Ondo Deputy Gov, Promises 100% Loyalty To Aiyedatiwa". Leadership. Retrieved 31 May 2024.
  3. 3.0 3.1 Kayode, Oyero. "Aiyedatiwa Nominates Ex-NASS Clerk Adelami As Deputy". Channels TV. Retrieved 31 May 2024. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  4. 4.0 4.1 "Adelami becomes deputy governor to Aiyedatiwa". 2 February 2024. Retrieved 14 September 2024. Cite error: Invalid <ref> tag; name "ondo" defined multiple times with different content
  5. Ojomo, Olufemi. "Olaide Adelami Sworn In As Ondo Deputy Governor". Channels TV. Retrieved 31 May 2024.
  6. Tope, Fayehun (1 February 2024). "Adelami Sworn In As Ondo Deputy Gov, Promises 100% Loyalty To Aiyedatiwa". Leadership. Retrieved 31 May 2024.