Lucky Aiyedatiwa
Ɗan siyasar Najeriya
Lucky Orimisan Aiyedatiwa (an haife shi 12 ga Janairu shekarar 1965) ɗan kasuwan Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya yi gwamnan jihar Ondo tun 2023.[1][2] Ya taɓa zama mataimakin gwamnan jihar Ondo daga shekarar shekarar 2021 zuwa 2023 a ƙarƙashin tsohon Gwamna marigayi Rotimi Akeredolu. Tsohon kwamishina ne a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).
Lucky Aiyedatiwa | |||
---|---|---|---|
24 ga Faburairu, 2021 - 27 Disamba 2023 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ilaje, 12 ga Janairu, 1965 (59 shekaru) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
A ranar 12 ga Disamba 2023, Aiyedatiwa ya zama muƙaddashin gwamna bayan tafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu yana hutun jinya. Ya taɓa riƙe muƙamin muƙaddashin gwamna daga watan Yuni zuwa Satumba 2023 a lokacin da Akeredolu yake hutun jinya.
Rayuwarsa ta farko
gyara sasheAn haifi Aiyedatiwa a ranar 12 ga Janairun shekarar 1965, ya fito ne daga Obe-Nla, al’ummar da ke da arziƙin man fetur a ƙaramar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Akeredolu, new deputy sworn in for second term". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2021-02-25. Retrieved 2021-04-06.
- ↑ "'Compete fairly' | The Nation Nigeria". thenationonlineng.net. Retrieved 2022-03-11.