Ola Oni
Ola Oni (an haife shi a shekarar ta 1933–ya mutu a ranar 22 ga watan Disamba shekara ta 1999) ya kasance masanin tattalin arzikin siyasa ne mai ra'ayin gurguzu kuma mai rajin kare hakkin dan Adam.[1][2]
Ola Oni | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Ekiti, 1933 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Mutuwa | Jahar Ibadan, 22 Disamba 1999 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Kehinde (mul) |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami, political economist (en) , gwagwarmaya da socialist (en) |
Employers | Jami'ar Ibadan |
Ya yi aiki a matsayin malami a Jami'ar Ibadan. Shi ne batun littafin tarihin rayuwar Ebenezer Babatope, mai suna Student Power in Nigeria (1991)[3].
Rayuwar farko
gyara sasheMai adawa ne da mulkin soja da kuma bin dimokiradiyya, Ola Oni ya fito ne daga Jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya inda aka haife shi amma yana zaune a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Najeriya[4]. Malamin ne a Jami’ar Ibadan amma an kore shi daga aiki saboda tsattsauran ra’ayin sa.[5] Littafin Ebenezer Babatope, "Student Power in Nigeria" (1956-198), ya faɗi rayuwar Ola Oni.[6] Ya mutu a ranar 22 ga watan Disamban, shekara ta 1999 a Asibitin Kwaleji na Jami’ar, garin Ibadan[7]. Bayan rasuwarsa, an saka wa cibiyar bincike ta zamantakewa, Comrade Ola Oni Center For Social Research don a rayar da shi.[8]
Rayuwar mutum
gyara sasheYa auri Kehinde Ola Oni, wata ma'aikaciyar gwamnati mai ritaya wacce yanzu ta makance.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Day Oshogbo Stood Still for Ola Oni, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 22 February 2015. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ Gugelberger, Georg M. (1986). Marxism and African Literature. google.nl. Africa World Press. ISBN 9780865430310. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ Mayer, Adam (2016). "Naija Marxisms: revolutionary thought in Nigeria". Journal of the African Literature Association. 12 (1): 93–100. doi:10.1080/21674736.2018.1430673.
- ↑ "From Oil Theft to Ola Oni's Valley in Ibadan (2) by Patrick Naagbanton | Sahara Reporters". Sahara Reporters. 2013-08-26. Retrieved 2017-10-20.
- ↑ Sanda, Laoye (2000). "Ola Oni's Struggle for Liberation". google.co.za. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ Adeoti, Gbemisola (October 2006). Intellectuals and African Development. google.nl. Zed Books. ISBN 9781842777657. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ "MY LIFE WITHOUT COMRADE OLA ONI -BLIND WIDOW". thenigerianvoice.com. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ "Towards immortalising Ola Oni". Daily Independent, Nigerian Newspaper. Retrieved 23 February 2015.
- ↑ Latestnigeriannews. "Twins of a kind". Latest Nigerian News. Retrieved 23 February 2015.