New African
New African Mujallar labarai ce da ake bugawa duk wata a cikin harshen turanci, daga London.[1] An fara buga ta tun shekara ta 1966, mutane da yawa suna karanta mujallar a faɗin nahiyar Afirka da ƴan ƙasashen waje na Afirka. Mujallar na da'awar ita ce mafi daɗewa da ake bugawa a kowane wata cikin harshen Turanci a Afrika, da kuma "jaridar da akafi siyarwar a nahiyar Afirka". Kamfanin IC Publications ne ke buga mujallar, haka zalika kamfanin ke buga mujallun; African Banker, New African Woman da kuma mujallar African Business.[2]
New African | |
---|---|
Mujalla | |
Bayanai | |
Farawa | 1966 |
Laƙabi | New African |
Muhimmin darasi | news magazine (en) |
Ƙasa da aka fara | Birtaniya |
Harshen aiki ko suna | Turanci |
Shafin yanar gizo | newafricanmagazine.com da exacteditions.com… |
Indexed in bibliographic review (en) | Scopus (en) |
Tarihi
gyara sasheAn kafa mujallar ne a shekarar 1966 da sunan African Development-(Cigaban Afirka). A cikin shekara ta 1977 an sauya sunan jaridar zuwa, New African Development, sunan da mujallar tayi amfani da shi zuwa shekara mai zuwa. A cikin 1978 an sake mata suna, idan ta koma sunan New African.[3]
Taro
gyara sasheDandalin Zuba Jari na COMESA
gyara sasheIC Publishing da mujallar New African sun yi aiki a matsayin masu masaukin baki da kuma tallata baje-kolin ciniki da zuba jari da/ko taro a madadin COMESA (Kasuwar gama-gari don Gabas da Kudancin Afirka). Musamman tarukan dandalin saka hannun jari na COMESA da aka gudanar a Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun kunshi shirye-shirye da kafofin watsa labaru masu yawa na goyon bayan Sinawa.[ana buƙatar hujja], "hannun" kudi na COMESA da ke kula da yarjejeniyoyin kasuwanci na COMESA da kuma saka hannun jari shine Babban Bankin Kasuwanci na Preferential Trade Area (Bankin PTA), wanda ba mamba na Afirka ba, kuma mafi girma da ba na yanki ba shine ƙasar Sin. .[ana buƙatar hujja]
Dandalin Kasuwancin AFRICA
gyara sasheHar ila yau IC Publishing ne mai shiryawa da kuma tallata taron kasuwanci na Afirka da Kudu maso Gabashin Asiya, taron kasuwanci na shekara-shekara wanda aka mayar da hankali kan dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka. Abin lura, babban mai tallafawa kuɗi na farko kuma mai goyon bayan dandalin AFRICASEA shine BRICS .
Sauran harsuna
gyara sasheA shekara ta 2007 IC Publications ya ƙaddamar da sabuwar mujjalar New African a cikin harshen Faransanci mai suna Le Magazine De l'Afrique ("Mujallar Afirka"), wadda ke nuna abubuwan da suka shafi Afirka a cikin harshen Faransanci. [4]
Jerin Iditoci/masu gyara-(editors)
gyara sashe- 1970 Maris-Yuli: Daraktan Edita - Richard Hall, Edita - Alan Rake
- 1970 Agusta: Edita - Alan Rake
- 1977 Janairu: Manajan edita - Alan Rake, Edita - Sam Uba, Mawallafi - Afif Ben Yedder
- 1978 Janairu-Afrilu: Babban Darakta - David Coetzee, Manajan edita - Alan Rake
- 1978 Mayu: Babban Edita - Peter Enahoro
- 1980 Janairu–Oktoba: Edita-Mawallafi - Peter Enahoro
- 1980 Nuwamba: Babban Edita - M. Mlamali Adam
- 1981 Fabrairu: Babban editan riko - Alan Rake, Mataimakin Edita - Baffour Ankomah
- 1995 Janairu: Babban Edita - Alan Rake, Mataimakin edita - Baffour Ankomah
- 1999 Yuli/Agusta: Edita - Baffour Ankomah
- 2018 Yuli/Agusta: Edita - Anver Versi
Manazarta
gyara sashe- ↑ Tokunbo Ojo (2016). "Framing of the Sino–Africa relationship in diasporic/pan-African news magazines". Chinese Journal of Communication. 9 (1): 38–55. doi:10.1080/17544750.2015.1049628. S2CID 142831334.
- ↑ "New African". New African Magazine. Retrieved 2021-01-05.
- ↑ "History of the Group" Archived 2013-09-22 at the Wayback Machine, IC Publications.
- ↑ ""New African, Le Magazine de l'Afrique"". Archived from the original on 2014-02-13. Retrieved 2023-02-28.