Alan Rake

Ɗan Jarida kuma marubuci

Alan Rake (an haife shi a shekara ta 1933) ɗan jarida ne a jaridar da ake bugawa da turanci, kuma marubuci game da Afirka.[1]

Alan Rake
Rayuwa
Haihuwa 1933 (90/91 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da marubuci

Farkon Rayuwa

gyara sashe

Alan Rake ya yi karatu a Jami'ar Oxford, inda ya karanci fannin: Falsafa, siyasa da tattalin arziki.[2] Jim Bailey ya gayyace shi, wanda kuma ya yi karatu a Oxford, don yin aiki da mujallar Drum.[3] A ƙarshen shekarar 1950 ya buɗe ofishin mujallar a birnin Nairobi, yana aiki a matsayin editanta jaridar ta Gabashin Afirka. A farkon 1960s ya ɗan yi aiki da mujjalar Drum a Afirka ta Kudu, kuma a matsayin Babban Manajan jaridar a Afirka ta Yamma,[4] kafin ya ci gaba da aiki da mujjalar Drum ɗin ta Gabashin Afirka a matsayin editan jaridar da ke Landan.[1]

A cikin 1968 ya kasance editan labarai na Africa Confidential a takaice.[5]

A cikin 1969 ya fara gyara a mujallar African Development da ake bugawa duk wata-wata daga Landan, daga baya aka sake mata suna izuwa New African. Ya kasance a can a matsayin edita har zuwa ritayarsa a shekarar 1999.[6]

  • (tare da John Dickie) Wanene a Afirka; shugabannin siyasa, soja da na kasuwanci na Afirka . London: Mai Saye da Kasuwanci na Afirka, 1973.
  • Wanene Wane a Afirka: shugabannin 1990s . Metuchen, NJ: Scarecrow Press, 1992.
  • Manyan Afirka 100 . Metuchen, NJ: Scarecrow Press, 1994.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Miranda H. Ferrara (2004). The Writers directory 2005. St. James Press. p. 1388. ISBN 978-1-55862-528-0.
  2. Alan Rake (2001). African Leaders: Guiding the New Millennium. Scarecrow Press. back cover. ISBN 978-0-8108-4019-5.
  3. Jim Bailey (1993). "Foreword". Kenya, the National Epic: From the Pages of Drum Magazine. East African Publishers. p. iv.
  4. "Contributors". Transition. 2 (4): 4. June 1962. JSTOR 2934806.
  5. "Africa Confidential: History". Retrieved 7 March 2021.
  6. Alan Rake (June 1999). "A Drum boy in Africa". New African. 375.