IC Publications

Kamfanin buga mujjalun Afrika da ke London, Ingila

IC Publications gidan buga mujjalu ne, wanda Afif Ben Yedder, ya kafa a cikin shekara ta 1957 a birnin Paris. Hedkwatar gidan a yanzu na cikin London Farringdon.

IC Publications
Bayanai
Iri kamfani
Ƙasa Birtaniya
Mulki
Hedkwata Landan
Tarihi
Ƙirƙira 1957
icpublications.com

Mutane miliyan 2.6 ne ke karanta rukunin mujallun kamfanin a cikin ƙasashe sama da 100.[1]

Da harshen Turanci, kamfanin na IC ke buga mujjalun; New African, Africam Business, Africam Banker, New African Woman, sai kuma a cikin harshen Faransanci, yake buga mujallun; Le Magazine De L'Afrique, Le Magazine Des Dirigeants Africains, Le Magazine De La Banque Et De La Finance da Femme Africaine . Babbar jaridar kamfanin itace, Mujallar African Business, mujallar da ake mutuntawa ga harkokin kasuwanci da zuba jari a duk faɗin nahiyar.

Manazarta gyara sashe

  1. "IC Publications". About Us. Archived from the original on 2013-03-12. Retrieved 2013-04-03.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe