Nafisat Abdullahi,[1] Asalin sunanta shi ne Nafisat Abdurrahman, Abdullahi Amma an fi saninta da Nafisat Abdullahi ko Kuma Nafisa Sai Wata Rana.[2][3][4] An haife ta a ranar 23 ga watan janairu a shekara ta alif Ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991.

Nafisat Abdullahi
Rayuwa
Haihuwa Jos, 23 ga Janairu, 1991 (33 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Jahar Kaduna
Karatu
Makaranta London School of Photography (en) Fassara
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a jarumi

Jaruma Nafisa ta fito a fina -finai da Dama irin su

Sai wata Rana

Madubin dubawa[5]

Burin Raina

Shiri mai Dogon zango Labarina

Ƴa Daga Allah,

An haifi jaruma Nafisat abdullahi a ranar 23 ga watan Janairu a shekara ta dubu ɗaya da ɗari Tara da casa'in da buyu 1992. Ta kuma fara karatun ta na secondary a garin Jos Kuma ta karasa a Abuja. A shekarar 2013 an dakatar da ita daga shirin fina finan kannywood saboda ta karya doka.[6][7]

Ta karanci theater art a jami,ar Jos, sannan ta karanci ilimin ɗaukan hoto a landan a makarantan ɗaukan hoto dake Birtaniya.

Nafisat abdullahi ta fara harkar film ne tun lokacin tana yar shekara sha takwas Kuma film ɗin da ya fito da ita shine SAI WATA RANA a shekara ta 2010 a ƙarƙashin kamfanin FKD PRODUCTION Wanda Ali Nuhu ya bada umarni. Ta bayyana a cikin wani najaerian film wato Nollywood Mai suna Blood and Heyna Wanda Kenneth Gyang ya bada umarni, tare da Ali Nuhu da Kuma Sadiq Sani Sadiq.

Ta fito a cikin fim ɗin da Aminu saira ya bada umarni wato ‘Ya daga Allah’ da kuma ‘Kalamu wahid’ a shekarar 2014.[8][9]

Fina finai.

gyara sashe
  • abarina Series [10]
  • Sai Wata Rana
  • Toron Giwa
  • Ummi
  • Zango
  • Ya daga Allah
  • Yar Agadez
  • Addini ko Al'Ada
  • Ahlul Kitab
  • Alkawarina
  • Alhaki Kwiukwiyo
  • Alhini
  • Allo (film)
  • Auren Tagwaye
  • Baban Sadik
  • Badi Ba Rai
  • Ban Kasheta Ba
  • Blood and Henna
  • Cikin Waye?
  • Dan Almajiri
  • Dan Marayan Zaki
  • Dare
  • Dawo Dawo
  • Farar Saka
  • Fataken Dare
  • Gabar Cikin Gida
  • Haaja
  • Har Abada
  • Jari Hujja
  • Laifin Dadi
  • Lamiraj
  • Madubin Dubawa
  • Guguwar So
  • Baiwar Allah.
  • Maimunatu

Lamban girma.

gyara sashe

Ta samu kyaututtukan girmamawa da dama irin su City People Entertainment Award 2013, sannan ta kasance jaruma ta ɗaya a masana'antar Kannywood a shekara ta dubu biyu da sha huɗu 2014. Jarumar ta karɓi kyautar girmamawa ta AMMA award a shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, MTN award a shekara ta dubu biyu da sha shida 2016, da Kuma Afro Hollywood award a shekara ta dubu biyu da sha bakwai 2017. Nafisa Abdullahi tayi soyyaya da Adam Zango har tayi burin aurenshi [11]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://x.com/NafisatOfficial?ref_src=twsrc%5Egoogle%7Ctwcamp%5Eserp%7Ctwgr%5Eauthor
  2. Team, 360hausa (2021-11-07). "BREAKING: Nafisat Abdullahi Launched "Nafcosmetics" As Her New Official Business". 360hausa.Com (in Turanci). Retrieved 2022-03-15.
  3. fynanse, fynanse (2023-08-24). "Nafeesat Abdullahi Biography And Net Worth". Nanablog.com.ng (in Turanci). Archived from the original on 2023-08-25. Retrieved 2023-08-25.
  4. "Nafisa Abdullahi Biography | Age | Net worth | Parent | Naijabiography". Naijabiography Media (in Turanci). Retrieved 2022-07-24.
  5. https://hausa.legit.ng/news/1467161-baki-da-ilimin-addini-fati-slow-ta-shigarwa-sarkin-waka-ta-yiwa-nafisa-abdullahi-wankin-babban-bargo/
  6. "Ku daina haihuwar 'ya'yan da ba za ku iya kula da su ba - Nafisa Abdullahi". BBC News Hausa. Retrieved 2022-08-04.
  7. http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/139399-kannywood-producers-suspend-star-actress-nafisa-abdullahi-for-organising-party.html
  8. http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/142503-kannywood-producers-lift-suspension-on-nafisa-abdullahi.html
  9. http://www.premiumtimesng.com/arts-entertainment/hausa-movies-arts-entertainment/185172-nafisa-abdullahi-confirms-romance-with-adam-zango.html
  10. "Wakokin Labarina Series". Archived from the original on 2022-02-12. Retrieved 2022-02-12.
  11. https://www.bbc.com/hausa/news/2015/06/150616_nafisah_abdullahi_kannywood