Nader Abd-Elmaksoud Fergany masani ne a fannin ilimin zamantakewa kuma masani a fannin ilimin tattalin arziki. Shi ne darektan cibiyar bincike ta Masar Al-Mishkat.[1][2]

Nader Fergany
Rayuwa
Haihuwa 20 ga Augusta, 1944 (80 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Alkahira
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki, sociologist (en) Fassara, Malami da demographer (en) Fassara
Kyaututtuka
Nader Fergany

An haifi Fergany a ranar ashirin 20 ga watan Agusta shekarar alif dubu daya da dari tara da arba'in da hudu 1944, a Giza. Ya sami digirinsa na farko a shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da ukku 1963 a tsangayar tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta Jami'ar Alkahira. Ya ci gaba da karatunsa a Jami'ar North Carolina kuma ya sami Ph.D. a shekara ta alif dubu daya da dari tara da saba'in 1970.[3]

Fergany da aka wallafa a fagen ilimin alƙaluma, ƙaura, kasuwar aiki, ilimi da ci gaba, a Masar da sauran ƙasashen Larabawa.[4]

Ya aiwatar da bincike don yawan cibiyoyi na Masar da na duniya. Shi ne mai ba da shawara ga ƙungiyoyin Larabawa da yawa da na duniya, kamar Cibiyar Tsare-tsare ta ƙasa, Majalisar Jama'a ta ƙasa, Hukumar Tattara da Ƙididdiga ta Tsakiya da Jami'ar Amurka, duk a Alkahira. Bugu da ƙari, ya yi bincike a Cibiyar Horarwa da Bincike a Ƙididdiga ta Larabawa a Bagadaza, Cibiyar Tsare-tsaren Larabawa a Kuwait da Kwalejin St Antony a Oxford a Birtaniya.[4][5]

Littattafai

gyara sashe

Fergany shine babban marubucin Rahoton Ci gaban Bil Adama na Larabawa na shekarar alif dubu biyu da biyu 2002. An girmama wannan rahoto a cikin shekarar alif dubu biyu da ukku 2003 tare da bashi lambar yabo ta Prince Claus daga Netherlands kuma shine farkon jerin rahotanni a cikin wannan filin da ya biyo baya a cikin shekaru masu zuwa. Masana kimiyya da yawa ne suka yi aiki da waɗannan rahotanni. [2] [6] Bugu da ƙari, ya wallafa (zaɓi):

  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da hudu 1974: An introduction to demographic analysis
  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da biyar 1975: The relationship between fertility level and societal development: And implications for planning to reduce fertility: an exercise in macro-statistical modelling
  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da daya 1981: The role of Egyptian labour in the construction sector in Kuwait
  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da bakwai1987: Differentials in labour migration, Egypt (1974-1984)
  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da daya 1981: Monitoring the condition of the poor in the third world: Some aspects of measurement
  • 2001: Human development and the acquisition of advanced knowledge in Arab countries : the role of higher education, research and technological development

Manazarta

gyara sashe
  1. Fergany, Nader (1970) On the macro-dynamic stochastic treatment of the size and age structure of a human population[permanent dead link] (his thesis in North Carolina)
  2. 2.0 2.1 El Amrani, Issandr (22 December 2004) Interview with the AHDR's Nader Fergany
  3. Istituto per gli Studi di Politica Internazionale, resume Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine
  4. 4.0 4.1 Bibliotheca Alexandrina, biography Archived 2009-02-26 at the Wayback Machine
  5. Fundación para las Relaciones Internacionales y el Diálogo Exterior, "biography". Archived from the original on June 12, 2012. Retrieved 2012-06-12.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  6. Prince Claus Award (2003) Jury report