Mohamed Salah Hamed Mahrous Ghaly (a Larabcin Misira محمد صلاح حامد محروس غالي) , an haifeshi a (15) ga watan yuni (1992), kwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Masar ne wanda yake buga wasa a gasar zakarun Turai da ƙungiyar Liverpool F.C. kuma yana bugawa a tawagar yan ƙwallon ƙasar Masar.

Muhammad Salah
Rayuwa
Cikakken suna محمد صلاح حامد محروس غالي
Haihuwa Nagrig (en) Fassara, 15 ga Yuni, 1992 (31 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Larabci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Magy Mohammed Sadek (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Al Mokawloon Al Arab SC (en) Fassara2010-20124412
  Egypt national football team (en) Fassara2011-unknown value9856
  FC Basel (en) Fassara2012-20147920
Chelsea F.C.2014-2015192
A.S. Roma (en) Fassara2015-20178334
  ACF Fiorentina (en) Fassara2015-2015269
  Liverpool F.C.2017-unknown value244154
 
Muƙami ko ƙwarewa wing half (en) Fassara
Ataka
winger (en) Fassara
Lamban wasa 11
Nauyi 71 kg
Tsayi 175 cm
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulmi

Salah ya fara ne daga buga ƙwallon sa na kwararru a ƙungiyar sa ta gida El'Makawloon a gasar kwararru ta ƙasar Masar (2011),daganan kuma sai ya wuce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel.A ƙasar Suwizalan, Salah ya samu nasarori da dama kamar (SAFP Golden Player award). Daga nan kuma Salah ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea F.C akan kwantaragin £11 milyan na yuro a shekarar 2014.Daga nan kuma sai Salah ya sauya sheka da ƙungiyar dake wasanta SERIE 'A' wato Fiorentina a kan kwantaragin £15 milyan na yuro.

Bayan nasarorin da ya samu a Rome Salah daga karshe ya koma ƙungiyar da yake taka leda a yanzu ta Liverpool F.C dake ƙasar Ingila akan kwantaragin yuro na miliyan £36.9,a shekarar 2017.[1]

Fara tashen sa gyara sashe

El Mokawloon gyara sashe

Salah a matsayin matashin ɗan ƙwallo a ƙungiyar El Makawloon. Sai ya shiga ƙungiyar kwararru ta ƙasar sa Masar.[2]

Besel gyara sashe

 
Salah na wasa da ƙungiyar Besel a Zenit St Petersburg a gasar UEFA Europa League a watan Maris na shekarar 2013

Salah ya kafa tarihi sosai a ƙungiyar Besel lokacin da yake buga masu wasa. Kamar a wasan da kungiyar sa ta buga filin wasa na Stadion Rankhof, Salah ya buga zagaye na biyun wasanne kawai amma saida yasamu damar zura kwallaye biyu a raga.[3]

Chelsea gyara sashe

A ranar 23 ga watan Janairu 2014 ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta fitar da sanarwar fara yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel kan yiwuwar komar salah kungiyar a kan kwantaragin yuro miliyan £11. A ranar 26 ga Janairu na 2014 ne kuma dai Chelsea ta sake fitar da sanarwar kammala yarjejeniyar ta su inda Salah yazama dan kasar Masar na farko da zai taka leda a Stamford Bridge. A ranr 8 ga Janairun na 2014 ne kuma Salah ya fara nuna bajintar sa a wasan ƙungiyar sa ta Chelsea da kuma ta Newcastle. Ranar 22 ga Maris 2014 Salah yaci ƙwallon sa ta farko a wasan Chelsea da Arsenal.[4]

 
Salah yana wasa da kungiyar Chelsea a Totrtenham Hotspur ranar 1 janairu shekarar 2015

Zaman bashi a Fiotentina gyara sashe

 
Salah yana wasa da kungiyar Fiorentin a shekarar 2015

Ranar 2 ga watan fabrairu na shekarar 2015 Salah yabar kungir kwallon kafa ta Chelsea zuwa kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina a matsayin bashi.

Roma gyara sashe

Ranar 6 ga watan Augusta shekarar 2015 Salah ya sake komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma a matsayin bashi.[5]

Liverpool gyara sashe

A ranar 22 ga watan yuni 2017 ne Salah ya sauya sheka Zuwa ƙungiyar sa ta liverpool akan kwantargin yuro miliyan £42.[6]


Taka leda a kulab gyara sashe

Salah ya fara buga wasa ne a kungiyoyin kwallo na matasa na cikin gida. Salah yakan yi rashin makaranta don yin tafiyar awa 3 don motsa jiki. [7] Dole ne a ba Salah abinci na musamman da kuma shirin horo saboda rashin cikar tsokoki saboda karancin shekarunsa.

Ko da yake yana samun lokacin wasa akai-akai, Salah ya yi nasarar cin kwallaye da dama.

Hotuna gyara sashe

 
Salah a wasan Liverpool da Manchester United a maris shekarar 2018
 
Salah daga hagu a wasan Masar da Tunusiya Augusta shekarar 2012

Manazarta gyara sashe

  1. Mohamed Salah" . Barry Hugman's Footballers. Retrieved 1 May 2018.
  2. Hossam Rabie (6 June 2018). "Egyptian soccer star's village has mixed feelings about native son" . Al-Monitor . Retrieved 20 March 2019.
  3. Abdelrahman, Mahmoud (3 January 2019). "Inside Salah's first club: A debut at 15, half-time tears & three-hour journeys to training" . Goal.com . Retrieved 18 January 2021.
  4. Trevor Haylett (3 May 2013). "Basel take heart after Chelsea defeat" . UEFA. Retrieved 3 May 2013.
  5. Fiorentina 1–2 Roma" . BBC Sport . 25 October 2015. Retrieved 25 August 2018.
  6. Critchley, Mark (30 June 2017). "Liverpool signing Mohamed Salah and Chelsea cleared of wrongdoing in Fiorentina loan court case" . The Independent. Retrieved 3 January 2021.
  7. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Early years