Liverpool F.C.
Liverpool Football Club kulob ɗin ƙwararrun ƴan ƙwallon ƙafa ne wanda ke zaune a birnin Liverpool a ƙasar Ingila, tana fafatawa a gasar Premier League, wanda shine babban gasa na nahiyar turai. Kulub ɗin ta samu nasarar lashe kofin turai na firimiya guda shida, fiye da ko wacce kulob a ƙasar ingila, UEFA Cups guda 3, UEFA Super Cup guda 3, 18 taken League , 7 Kofin FA, a tarihi 8 League Cups, da kuma Garkuwan jama'a na FA guda goma sha biyar (15).
Liverpool F.C. | |
---|---|
You'll Never Walk Alone (en) | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Liverpool Football Club |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Birtaniya |
Laƙabi | The Reds da The Scousers |
Mulki | |
Shugaba | Tom Werner (en) |
Hedkwata | Liverpool |
Mamallaki | Fenway Sports Group (en) |
Sponsor (en) | Standard Chartered (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 3 ga Yuni, 1892 |
Wanda ya samar |
John Houlding (mul) |
Awards received | |
|
Tarihi
gyara sasheAn kafa ta a 1892, kulob ɗin ya shiga cikin Kungiyar kwallon kafa na firimiya A shekarar da ta biyo baya, kuma tana wasannin ta ne a 'Anfield' tun da a ka kafa ta. Liverpool ta zamar da kanta babban kulob a nahiyar turai a shekarun 1970s da 1980s sanda Bill Shankly da Bob Paisley suka jagoranci ƙungiyar samun nasara a taken 'League' guda goma sha ɗaya (11) da seven da kofukan turai. A karkashin jagorancin Rafael Benítez da kaftin Steven Gerrard, Liverpool ta zama zakaran turai a karo na biyar a shekara ta 2005.
Liverpool itace ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta tara makudan kudade a duniya a 2016–17, da kudin shiga a shekara da suka kai €424.2 miliyan,[1] kuma ita ce na takwas mafi darajan kulub a duniya a 2018, da kudin da suka kai $1.944 biliyan.[2][3] Liverpool na da babban hamayya sosai tsakanin ta da Manchester United da kuma Everton.
Magoya bayan kulub din su biyu suna shiga cikin alhini, tare da mutane 39 – wanda yawancin su Italiyawa ne da magoya bayan Juventus suka mutu, hakan yasa a ka hana Kungiyoyin ingila shiga ko wacce irin gasa a Turai na tsawon shekara biyar, da kuma Bala'i na 'Hillsborough' a 1989, inda magoya bayan Liverpool 96 suka mutu a murkushe shingen kewaye.
Kungiyar ta canja kayan tsawarta daga Jan Riga da farin wando zuwa Jan kafa a shekarar 1964 kuma tun daga nan shi take amfani dashi har a yau. Taken kulob din shine "You'll Never Walk Alone" (bazaka taba tafiya kai kadai ba.)
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Deloitte Football Money League 2018". Deloitte. 23 January 2018. Retrieved 23 January 2018.
- ↑ Ozanian, Mike. "The World's Most Valuable Soccer Teams 2018". Forbes. Retrieved 2018-06-12.
- ↑ "How Liverpool's worldwide fanbase will be tuning into events at Manchester United". Liverpool Echo. Retrieved 29 July 2018.