Mohammed Bencheneb (26 Oktoba 1869 – 5 Fabrairu 1929) farfesa ne ɗan Aljeriya, marubuci kuma masanin tarihi. [1]

Mohamed Bencheneb
Rayuwa
Haihuwa Médéa (en) Fassara, 26 Oktoba 1869
ƙasa Faransa
Mutuwa Aljir, 5 ga Faburairu, 1929
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a marubuci da Malami
Muhimman ayyuka tḥfẗ al-ādb fī mīzān ašʿār al-ʿrb (en) Fassara
Mamba Académie des sciences d'outre-mer (en) Fassara
Arab Academy of Damascus (en) Fassara
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haife shi a cikin shekarar 1869 iyayen sa 'yan asalin Turkawa ne, [2] Bencheneb ya zama malami daga shekarun 1889, yana da kwarewa a harsuna da yawa, ban da Larabci da Faransanci, ya koyi Latin, Ingilishi, Italiyanci, Sifen, Jamusanci, Farisa da Turkish. [3] Bencheneb ya koyar a Makarantar Graduate Arts na Algiers kafin a tura shi a shekarar 1898 zuwa farfesa a Madrasa na Constantine inda ya zauna na shekaru uku. Ya koma Algiers a 1901 a matsayin farfesa, ya koyar tun a shekarar 1904 a Madrasa Thaalibia, kuma a cikin shekarar 1908 yana da alhakin manyan tarurrukan ilimi. Ya buga kasidu da dama: ɗaya daga cikin kasidunsa na farko yana cikin Revue Algerienne de Droit ("Journal of Algerian Law") a shekara ta 1895, sannan a cikin Revue Africaine ("Jarida ta Afirka") inda aka ɗauki nauyin yawancin labaransa. [3]

Bayan mutuwarsa a shekara ta 1929, an binne shi a makabartar Thaalibia na Casbah na Algiers.

Bibliography

gyara sashe
  • Cheurfi, Achour (2001), La Classe Politique Algérienne (de 1900 à nos jours): Dictionnaire Biographique, University of Michigan, ISBN 9961-64-292-9.


  • Déjeux, Jean (1984), "Bencheneb, Mohamed", Dictionnaire des Auteurs Maghrébins de Langue Française, Karthala, ISBN 2865370852.


  • Oulebsir, Nabila (2004), "Bencheneb, Mohamed", Les usages du patrimoine: Monuments, musées et politique coloniale en Algérie, 1830-1930, Editions MSH, ISBN 2735110060.

 

Manazarta

gyara sashe
  1. Déjeux 1984.
  2. Cheurfi 2001.
  3. 3.0 3.1 Oulebsir 2004.