Turkanci yare ne na dangin harsunan Turkic, wanda mutane miliyan goma zuwa goma sha biyar ke da shi a matsayin harshen uwa, mafi yawancin su a Kudu maso gabashin Turai, da wasu miliyan sittin zuwa sittin da biyar a yammacin Asiya (mafiya yawa a Anatoliya). Ana samun Turkawa a wasu kasashen na wajen Turkiya kamar Jamani, Bulgariya, Arewacin Macedoniya, Kudancin Cyprus, Girka, Caucus da sauran sassan Turai da Tsakiyar Asiya. Kasar Cyprus ta taba rokar kungiyar taraiyar Turai ta saka harshen Turkaci cikin jerin harsunan gudanarwar ta.

Turkanci
Türkçe
'Yan asalin magana
harshen asali: 82,231,620 (2021)
second language (en) Fassara: 5,870,300 (2021)
harshen asali: 79,526,830 (2020)
harshen asali: 79,400,000 (2019)
harshen asali: 78,527,240 (2012)
harshen asali: 71,435,850 (2006)
second language (en) Fassara: 5,670,300 (2020)
second language (en) Fassara: 350,000 (2006)
second language (en) Fassara: 380,300 (2006)
Turkish alphabet (en) Fassara, Baƙaƙen larabci, Baƙaƙen boko da Arabic script (en) Fassara
Lamban rijistar harshe
ISO 639-1 tr
ISO 639-2 tur
ISO 639-3 tur
Glottolog nucl1301[1]

Tarihi gyara sashe

Turkanci yankin Turtic ne da ahalin harsunan Altaic.Turkanci na da yanayin furuci kamar na harshen Finnish da Hungarian.

Ana amfani da haruffan larabci wajen yin rubutun harshen Turkanci tun a wajajen shekarar 900 miladiyya zuwa shekara ta 1928. Daga baya kuma sai Mustafa Kemal Atatürk ya canja shi zuwa yin amfani da haruffan Boko. Sakamakon saukin koyo na haruffan Boko da kuma wahalar koyo na haruffan Larabci sai gwamnatin kasar turkiya ta maida yin amfani da haruffan boko a hukumance. Haruffan Turkanci sun samo asali ne daga haruffan boko ana amfani dasu wajen rubuta harshen Turkanci, sun kunshi haruffa 28 wanda bakwai daga cikinsu sun bambanta ta wajen rubuta su sakamakon yanayin furucin su. Sune kamar haka (Ç, Ğ, I, İ, Ö, Ş, and Ü).

Wannan harshen ya yi kamanceceniya da sauran harsunan Turtic irin su Azerbaijani, Turkmen, Uzbek da Kazakh.

Misalai gyara sashe

  • Merhaba = Barka
  • Selam = Sallama
  • Nasılsın? = Ya kake?
  • İyiyim = Ina Lafiya
  • Teşekkür ederim = Nagode
  • Teşekkürler = Godiya
  • Sağol = Nagode maka
  • Benim adım .... = Sunana shi ne...
  • Türkçe bilmiyorum. = Ban san turkanci ba
  • İngilizce biliyor musunuz? = Kasan Turanci?
  • Tekrarlar mısınız? = Zaka iya maimaitawa?
  • Evet = E
  • Hayır = A'a
  • Belki = Watakila
  • Biraz = Karami
  • Acıktım = Ina jin yunwa
  • Dur! = Tsaya!
  • Yapma! = Kada kayi!
  • İstemiyorum. = Bana so
  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Turkanci". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.