Mike Ozekhome

Lauya ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama

Mike Agbedor Abu Ozekhome (an haife shi ranar 15 ga watan Oktoba, a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da bakwai 1957A.C)a Iviukwe, Agenebode a cikin jihar Edo, Nigeria ) lauya ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, wanda ke riƙe da muƙamin Babban Lauyan Najeriya.[1] An san shi da aikinsa a matsayin lauyan tsarin mulki[2] da kuma mai magana.[3]

Mike Ozekhome
Rayuwa
Haihuwa jahar Edo, 15 Oktoba 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yaren afenmai
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya
Harsuna Turanci
Yaren afenmai
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam, constitutional lawyer (en) Fassara da orator (en) Fassara
Mike Ozekhome
Mike Ozekhome

Mike Agbedor Abu Ozekhome ya samu digirinsa na farko a fannin shari'a (LL. B.) daga Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife (a lokacin, wacce aka fi sani da Jami’ar Ife), ya kammala a shekarar 1980. Sannan ya halarci Makarantar Shari'a ta Najeriya, Victoria Island Lagos (1981). Tsohon Cif Kanmi-Isola Osobu ya kasance mai ba shi shawara ga almajiri bayan shigarsa Lauyoyin Najeriya a watan Yuli, 1981.[4] Bayan haka, ya koma Jami'ar Obafemi Awolowo don samun digiri na biyu a fannin shari'a (LL. M.), ya sami digirin a shekara ta 1983.[5]

Kafin ya sami LL. M., Ozekhome an tura shi ne zuwa ma’aikatar shari’a ta Yola a matsayin mamba a hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) sannan kuma zuwa ma’aikatar shari’a ta tarayya, jihar Legas. Daga nan kuma ya zama lauyan gwamnati na asusun bayar da tallafi na ƙasa (National Social Insurance and Trust Fund (NSITF).[6][7]

Daga nan sai ya shiga zauren babban lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama kuma mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, marigayi Cif Gani Fawehinmi, inda a hankali ya tashi ya zama mataimakin shugaban majalisar, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1985. Ya kafa kamfaninsa na ofisoshi da yawa, Mike Ozekhome's Chambers, a cikin 1986.[7][8] A shekarar 2010, ya kasance ɗaya daga cikin manyan malaman shari'a 19 da aka ba su muƙamin Babban Lauyan Najeriya.[2][9]

Garkuwa da saki

gyara sashe

An yi garkuwa da Ozekhome a kan babbar hanyar Benin-Auchi a ranar 23 ga watan Agustan 2013 kuma an kama shi domin neman kuɗin fansa.[10][11][12][13] An kashe ƴan sanda huɗu da ke mayar da martani a kokarin su na daƙile afkuwar garkuwar.[11] Garkuwar da shi da aka yi, ya ja hankalin kafafen yaɗa labarai da dama. [14][15][16] An kama Ozekhome tare da kusan wasu mutane goma sha biyu a cikin abin da ya bayyana a matsayin sansani mai tsari, an saki Ozekhome bayan makonni da yawa lokacin da aka tattauna batun kuɗin fansa da masu garkuwa da mutane, ya dawo gida ranar 12 ga watan Satumba 2013.[12][17] A ranar 25 ga Satumba, 2013, rundunar sojojin Najeriya da jami'an DSS sun kama mai laifin Kelvin Prosper Oniarah da ake nema ruwa a jallo.[18]

Manazarta

gyara sashe
  1. Ibekwe, Nicholas (24 August 2013). "Radical Lawyer Mike Ozekhome Kidnapped". The Premium Times. Retrieved 13 July 2014.
  2. 2.0 2.1 Ige, Ise-Oluwa (2 February 2010). "Ozekhome, Ogunba, Pinheiro 16 others make SANs list". Vanguard. Retrieved 13 July 2014.
  3. "Chief Mike Ozekhome, SAN". Tribune Online (in Turanci). 2022-03-02. Retrieved 2022-03-17.
  4. Mike Ozekhome's Chambers's Website "Welcome to MIKE OZEKHOme's CHAMBERS". Archived from the original on 2014-07-14. Retrieved 2014-06-17.
  5. "About Mike"
  6. "Citation". Mike Ozekhome. Archived from the original on 14 July 2014. Retrieved 13 July 2014.
  7. 7.0 7.1 National Mirror, "This life is vanity, empty, says Ozekhome (SAN) @ 55" "This life is vanity, empty, says Ozekhome (SAN) @ 55 | National Mirror". Archived from the original on 2014-07-14. Retrieved 2014-06-15.CS1 maint: unfit url (link)
  8. National Mirro, "Mike Ozekhome (SAN): Out of kidnappers’ den" "Mike Ozekhome (SAN): Out of kidnappers' den | National Mirror". Archived from the original on 2014-05-31. Retrieved 2014-06-17.CS1 maint: unfit url (link)
  9. "OZEKHOME, OGUNTADE, EKOMARU, 16 OTHERS BECOME SANS : NIGERIA GENERAL TOPICS, FREE, WEBSITES, INTERNET, SOCIETY, REAL ESTATES, BUSINESS" (in Turanci). Retrieved 2019-08-12.
  10. "Gunmen kidnap prominent lawyer in southern Nigeria". AFP (in Turanci). 2015-03-25. Retrieved 2019-08-12.
  11. 11.0 11.1 Ibekwe, Nicholas (2013-08-24). "Radical lawyer, Mike Ozekhome, kidnapped - Premium Times Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2019-08-12.
  12. 12.0 12.1 Aninkuotu, Eniola (13 September 2013). "Ozekhome home, recounts ordeal in kidnappers' den". Punch. Archived from the original on 16 September 2014. Retrieved 14 July 2014.
  13. "Nigerian human rights lawyer Mike Ozekhome abducted". tvcnews.tv. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 4 December 2021.
  14. "Gunmen kidnap prominent lawyer in southern Nigeria". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2019-08-12.
  15. Latestnigeriannews. "Ozekhome's kidnap". Latest Nigerian News (in English). Retrieved 2019-08-12.CS1 maint: unrecognized language (link)
  16. The Vanguard, "More reactions trail Ozekhome’s kidnap"
  17. "Ozekhome Admits Paying Ransom For Release". The ICIR (in Turanci). 2013-11-04. Retrieved 2019-08-12.
  18. The Vanguard, DSS, Army arrest Mike Ozekhome’s kidnapper.