Michael Otedola
Michael Otedola (an haife shi a ranar16 ga watan Yuni shekarar 1926 - 5 May 2014) ya kasance ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Najeriya.
Michael Otedola | |||
---|---|---|---|
ga Janairu, 1992 - 18 Nuwamba, 1993 ← Raji Rasaki - Olagunsoye Oyinlola → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Epe, 16 ga Yuli, 1926 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Mutuwa | Epe, 5 Mayu 2014 | ||
Makwanci | jahar Legas | ||
Ƴan uwa | |||
Yara |
view
| ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Westminster (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Babban taron jam'iyyar Republican |
Otedola an haife shi ne a ranar 16 ga watan Yuni shekarar 1926 a cikin dangin musulmai a Odoragunsin, karamar hukumar Epe ta jihar Legas. Ya kuma mutu a ranar 5 ga Mayu 2014 a gidansa da ke garinsa na Epe, Legas.
Rayuwar farko
gyara sasheBayan ya koma Legas ya cigaba da karatunsa sai ya sami gurbin karatu a fannin koyon aikin jarida a makarantar Regent Street Polytechnic da ke Landan inda ya kammala a shekarar 1958.
Ya fara aikinsa na malami kafin ya yi aiki a matsayin mai kawo rahoto a jaridar St. Pancras Chronicle, sannan a matsayin mai kawo rahoto sannan daga baya ya zama karamin edita a The Guardian da The Times a Ingila.
Siyasa
gyara sasheBayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1959 ya zama Jami'in yada labarai a gwamnatin Yammacin Najeriya, kuma yayin wannan mukamin an nada shi Editan jaridar Western Nigeria Illustrated. A shekarar 1961 sannan ya koma cikin hulɗa da jama'a, yana aiki da Western Nigeria Television / Western Broadcasting Service (1961-1964) da Mobil Oil Group of Companies (1964-1977), ya ci gaba a matsayin mai ba da shawara ga Mobil bayan barin kamfanin.
An zabe shi gwamnan jihar Legas daga shekarar 1992 zuwa shekara ta 1993 a karkashin kungiyar National Republican Convention (NRC), ya bar mulki lokacin da Janar Sani Abacha ya hau mulki. Gwamnatinsa ta taimaka wajen kafa kwalejin Kwalejin Fasaha ta Yaba a Epe, garin haihuwarsa.
Bayan ya bar ofis, ya ci gaba da aikinsa na marubuci, mai ba da shawara mai rike da mukamai a kan allunan kamfanoni daban-daban, da kuma taimakon jama'a. A watan Fabrairun shekarar 2010 jaridar ThisDay ta ba da sanarwar cewa yana daga cikin fitattun 'yan Najeriya 15 da suka ci kyautuka a rayuwa. Dansa Femi Otedola ya zama hamshakin attajiri wanda ya mallaki katafaren kamfanin mai na Najeriya Zenon Petroleum and Gas Limited. Makarantar Koyon Firamare ta Michael Otedola an sanya mata sunansa ne bayan rasuwarsa.