Masarautar Karaye
Masarautar Karaye masarauta ce a jihar Kano mai hedikwata a garin Ƙaraye. Sarkin Ƙaraye na yanzu shine Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.[1][2][3]
Masarautar Ƙaraye | ||||
---|---|---|---|---|
Emirate (en) | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 2019 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Babban birni | Karaye | |||
Dissolved, abolished or demolished date (en) | 23 Mayu 2024 | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano |
Tarihi
gyara sasheGarin Ƙaraye hedikwatar masarautar Ƙaraye ce kuma tana yammacin birnin Kano. Tun kafin zuwan Bagauda a shekarar 999, Magurguji ke zaune a Karaye. An kafa garin Ƙaraye a shekara ta 1085. Daga shekarar 1101 zuwa 1793, sarakunan Habe sun yi sarautar Ƙaraye. A zamanin sarakunan Habe, masarautar Karaye ta kara faɗaɗa zuwa yankin Yamma da Arewacin Jihar Kano da ke yanzu.[4]
Dangantaka da Kano
gyara sasheA lokacin da Majalisar Bagauda ke mulki a Kano sun nemi haɗin kan maƙwabciyarsu Masarautar Karaye domin haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kare kansu daga wasu masarautu irinsu Zariya da Katsina da Sakkwato . Ƙaraye ta amince ya bada hadin kai da gidan Bagauda inda Ƙaraye ya koma masarautar Kano . Daga lokacin da Karaye yake ƙarƙashin masarautar Kano har zuwan Sarakunan Fulani bayan Jihadin Usman Dan Fodio.[5]
Masarautar Ƙaraye A Yanzu
gyara sasheMasarautar Ƙaraye ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin Daular Kano har zuwa shekarar 2020 lokacin da gwamnatin jihar Kano ta fitar da wasu sabbin masarautu guda biyar tare da sauya tsarin masarautar Kano. A wancan lokacin gwamnatin Kano ta dawo da sabuwar Masarautar Karaye.[6][7][8][9] Masarautar Ƙaraye ta ƙunshi ƙananan hukumomi takwas na jihar Kano, Karaye, Rogo, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi, Kiru da Shanono.[10]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ Lawal, Muhammad Dahiru (2021-06-11). "Karaye Emirate - A Symbol of Hope and Prosperity". Arewa Agenda (in Turanci). Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "Emir of Karaye Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "Dr. Ibrahim Abubakar II Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "Alakar Masarautar Karaye da Gidan Dabon Kano". Aminiya (in Turanci). 2019-05-10. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ Fika, Adamu Mohammed (1978). The Kano Civil War and British over-rule, 1882-1940. Ibadan: Oxford University Press. ISBN 978-154-008-7. OCLC 5246776.
- ↑ "Why we created more emirates in Kano -Ganduje | The Nation Newspaper" (in Turanci). 2021-05-16. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "4 Emirates create to transform society- Karaye Emir". TRIUMPH NEWS (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "Ganduje's Creation Of Kano Emirates Was To Carry Everyone Along, Says Bayero". Channels Television. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "Ganduje approves 4 new emirates in Kano". Daily Trust (in Turanci). 2019-05-09. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ Buhari, Mustapha (2019-05-08). "Emir of Kano now controls 8 LG district heads as Assembly creates 4 more emirates". Daily Nigerian (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-30. Retrieved 2022-12-30.