Masallacin At-Taqwa ( Chinese ) wani masallaci ne a garin Dayuan, Gundumar Taoyuan, Taiwan. Shine masallaci na bakwai kuma na kwanan nan a ƙasar Taiwan. An gina masallacin a shekarar 2013.

Masallacin At-Taqwa
Wuri
Island country (en) FassaraTaiwan
Special municipality (en) FassaraTaoyuan
District of Taiwan (en) FassaraDayuan District (en) Fassara
Coordinates 25°04′02″N 121°10′49″E / 25.067211°N 121.180358°E / 25.067211; 121.180358
Map
History and use
Opening9 ga Yuni, 2013
Suna saboda Taqwa (en) Fassara
Addini Musulunci
Launi ██ Fari
Faɗi 5 meters
Tsawo 26 meters
Contact
Address 桃園市大園區自立一街8-2號
Waya tel:+886-3-384-0539
Offical website
Masallacin At-Taqwa

Wasu ma'aurata 'yan asalin kasar Indiya ne suka fara gina masallacin waɗanda suke da shagon Indonesiya a kusa da Dayuan. Ma'auratan sun sayi fili kusa da shagonsu don gina masallaci. Bayan tattara duk kudaden da ake buƙata domin yin masallacin, daga ƙarshe aka gina masallacin kuma aka buɗe shi a ranar 9 ga Yunin 2013.

Kafa masallacin ya nuna cewa yawan Musulmai na ƙaruwa a Taiwan, inda da yawansu ke aiki a masana'antu, kantuna ko gidaje . Yawancin waɗannan Musulman sun fito ne daga Indonesia. Ana iya ɗaukar wannan azaman ƙaura ta huɗu ta musulmai zuwa Taiwan.

Gine-gine

gyara sashe

Yankin masallacin yana da murabba'in mita 130. Yana da hawa uku, inda ya kunshi zauren salla maza, zauren salla mata, dakin tsammani, azuzuwa da dakunan kwanan dalibai.

Manazarta

gyara sashe