Masa

Waina abinci ne mai sauƙi wanda kuma aka sani da Masa. Tasa ce da za a iya shirya ta da farin Masara ko Rice na gida. An fi shirya ta a Arewacin Najeriya kuma ana cin ta tare da Miyan Waina/Taushe.

Masa abinci ce wacce aka fi sani da suna Waina. Kuma yana ɗaya daga cikin abincin gargajiya, Musamman a ƙasar Hausa. Abinci ne wanda aka fi cin shi da safe kuma ana cin shi a koda yaushe.

Masa
Tarihi
Asali Najeriya
ana yin waina da gero
Sa hoto[1]

Yadda ake haɗa shi shi ne: da shinkafar tuwo da kuma "yeast" da dai sauransu. Akan ci shi ne da miyar taushe. Ana kuma iya cin shi haka nan, musamman idan aka sa masa sukari. Mutanan jihar Bauchi suna da kwarewa a kan harkar masa wato waina. [2][3][4] Sannan masa iri uku ce, akwai masa ta zallar masara, akwai kuma masa ta zallar Shinkafa, akwai kuma wadda ake hada shinkafa da masara, akwai kuma masar gero. Ana cin ta da garin kuli-kuli yana da dadi sosai.

Mace tana tuyar masa

Bibiliyo gyara sashe

  • Adamu, Abdalla Uba, shekara ta alif dari tara da hamsin da shida 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
  • Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2

Manazarta gyara sashe