Maimuna Waziri

Yar boko a Najeriya

Farfesa Maimuna Waziri (an haife ta ne a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1966). Malamar Jami'a ce, Farfesar Ilimin Kimiyyar Sinadarai kuma mace ta farko da ta fara zama mukaddashiyar shugabar jami’ar Gwamnatin Tarayya dake garin Gashua inda aka tabbatar da shugabancinna ta a ranar goma sha shida 16 ga watan Janairun 2021.[1]

Maimuna Waziri
Rayuwa
Haihuwa 28 Oktoba 1966 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar Yobe
Jami'ar Ibadan
Jami'ar Maiduguri
Matakin karatu Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da researcher (en) Fassara
Employers Jami'ar Tarayya, Gashua
Imani
Addini Musulunci

Tarihin Rayuwarta da Karatu

gyara sashe

An haifi Maimuna Waziri ce a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1966 a garin Gashuwada ke karamar hukumarBade. Ta kammala Firamare a Central Primary School, a shekarar alif ɗari tara da saba'in da ɗaya 1971-zuwa 1975 da kuma Sakandandarenta GSS tsakanin shekara ta alif ɗari tara da saba'in da biyar 1975 zuwa alif ɗari tara da tamanin 1980 dukka da suke garin Gashuwa. Ta kuma halacci jami’ar Bayero University Kano (BUK) da ke Kano inda ta samu shaidar digirinta na farko a fannin ilimin Sinadarai a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da ɗaya 1981-zywa alif ɗari tara da tamanin da shida 1986. Saboda tsayuwarta da jajircewarta wanda ya sa ta tsaya kyam a tsakanin sauran mata, Maimuna ta ci gaba da karatun digirinta na biyu a wannan sashen a Jami’ar Ibadan a a cikin shekara ta alif ɗari tara da tamanin da takwas 1988 inda ta kammala a Shekara ta alif ɗari tara da casa'in 1990. Sannan ta yi digirin-digirgir dinta a bangaren nazarin Sinadirai a Jami’ar Maiduguri a shekara ta dubu biyu da shida 2006.[2] Ta fara karantarwa ne a jami’ar Maiduguri a matsayin mataimakiyar Malama a Shekara ta alif ɗari tara da tamanin da bakwai 1987 bayan ta kammala Digirinta na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano inda ta karanci sashen Sinidirai. Sha’awarta ga koyarwa ya sa ta ci gaba da karantarwa a sashen nazarin Sinadarai na jami’ar Maiduguri a matsayin babbar Malama. Duk da kasancewarta Malama ce a bangaren nazarin Sinadarai, hakan bai hana Maimuna shiga a dama da ita a sha’anin gudanar da mulki a Nijeriya ba; domin kuwa a shekarar alif ɗari tara da tamanin da bakwai 1987 aka nada ta Kwamishinar harkokin mata da ci gaban zamantakewa daga bisani ta zama Kwamishinar kasuwanci da harkokin ma’aikatu daga shekarar alif ɗari tara da casa'in da takwas 1998 zuwa alif ɗari tara da casa'in da tara 999 dukkanin wadannan mukaman a jihar Yobe ta rike su. Har ila yau ta zama mataimakiya ta musamman ga Gwamna akan harkokin ci gaban ayyuka daga shekarar alif ɗari tara da casa'in da tara 1999 zuwa shekara ta dubu biyu da ɗaya 2001. Sannan ta zama Daraktan kimiyya da fasaha, a ma’aikatar hukumar ilimi da ke Damaturu, daga shekarar dubu biyu da ɗaya 2001 zuwa dubu biyu da bakwai 2007.

Gudummawa

gyara sashe

Farfesa maimuna Waziri tana kuma daga cikin wadanda aka baiwa hakkin samar da jami’ar jihar Yobe bayan an samar da jami’ar a shekarar dubu biyu da bakwai 2007, ta karantar a matsayin babbar Malama a sashen nazarin Sinadarai, a lokaci guda kuma ta zama Darakta a makarantar sharar fagen shiga jami’a, sannan ta zama shugabar Tsangayar kimiyya da fasaha daga shekara ta dubu biyu da bakwai 2007 zuwa shekara ta dubu biyu da tara 2009 a wannan jami’ar ta jihar Yobe.

Lambar Yabo

gyara sashe

Ta karbi kyaututtukan girmamawa daban-daban wadanda suka hada da kyautar tunawa da Michael Collins ta sashen Sinadarai a shekarar alif ɗari tara da tamanin da huɗu 1984, sannan da kyautar wanda ya fi kwazo ta tunawa da Michael Collins a sashen Sinadarai a jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar alif ɗari tara da tamanin da shida 1986. Ta kuma samu lambar yabo mai daraja na ‘Waye Ne Ba Baye Ba’ (Who is who) a sashen ilimin kimiyya da fasaha ta Afrika, da sauran wasu kyaututtuka daban-daban wadanda suka daga lifafarta taccilla sama har ta kasance kallabi a tsakanin rauwuna.

Kungiyoyi

gyara sashe

Maimuna waziri member ce a kungiyar nazarin Sinadarai ta Nijeriya da wasu kwararrun kungiyoyi wanda suka hada da Cibiyar kwararru ta ‘Chartered Chemist’ ta Nijeriya, sai wata cibiyar mata kwararru ta binciken kimiyya da fasaha ta hadin guiwa ta duniya da kasashen masu tasowa. Ta sadaukar da rayuwarta gaba daya wajen neman Ilimi da bincike da karantarwa, sannan ta yi aiki a wurare daban-daban wanda suka hada da jami’ar Maiduguri da jami’ar Bukar Abba Ibrahim dake jihar Yobe (Jami’ar Jihar Yobe a yanzu) da ke garin Damaturu, daga nan ta koma jami’ar Tarayya da ke garin Gashuwa inda aka ƙara mata girma zuwa matsayin Farfesa daga ranar 1 ga watan Oktoban na shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015, kuma ita ce Farfesa ta biyu a dukkanin fadin jihar Yobe a cikin matan jihar wannan dalilin ne ya sanya ta zama madubi a tsakanin matan jihar da kuma na kasar Nijeriya baki ɗaya. Kafin zamanta mukaddashiyar shugaban jami’ar Gashua gaba daya, Farfesa Maimuna Waziri ta rike mukamin Mataimakiyar shugaban sashin gudanarwa na jami’ar tarayya da ke Gashuwa da ke jihar Yobe, bisa himmarta ne yanzu ta zama shugaba a jami’ar gaba daya, ta karbi ragamar jami’ar ne daga hannun Farfesa Andrew Haruna wanda wa’adin kammala aikinsa ya kare a ranar 10 ga watan Fabrairun.[3] Bayanai sun zo ma wannan shafin cewa Farfesoshi 48 ne suka nemi shugabantar jami’ar amma uku ne kacal suka samu zuwa matakin karshe na tantancewa wanda aka zabi Farfesa maimuna Waziri daga karshe.[4] Farfesa Maimuna Waziri wacce ta kasance ita ce mace ta biyu a dukkanin fadin jihar Yobe da ta zama Farfesa bayan da ta jajirce da neman iimi da kuma sallamawa sha’anin neman iimi, maca ce mai son ganin iimin mata ‘yan uwanta ya bunkasa, wannan dalilin ne ma ya sanya ta samu kanta cikin jerin matayen da suke dafa wa sha’anin karatun mata musamman a jihar ta da kuma kasa baki data. Farfesa Waziri mamba ce a kungiyar nazarin sinadarai ta Nijeriya da wasu kwararrun kungiyoyi wanda suka hada da Cibiyar kwararru ta ‘Chartered Chemist’ ta Nijeriya, sai wata cibiyar mata kwararru ta binciken kimiyya da fasaha ta hadin guiwa ta duniya da kasashen masu tasowa ta kuma kasance mace wacce ta samu shiga jerin fitattun mata ne bayan da ta jajirce wajen ganin ilmi ya bunkasa a tsakanin matan kasar nan, hakan ya sa ta shiga kungiyoyi da dama domin taimakawa.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2024-05-20. Retrieved 2022-05-17.
  2. https://www.channelstv.com/2021/01/16/female-professor-emerges-vice-chancellor-at-yobe-university/
  3. https://dailypost.ng/2021/12/05/yobe-sets-up-committee-to-source-manage-funds-to-boost-education-sector/
  4. https://www.vanguardngr.com/2021/01/lawan-congratulates-new-vice-chancellor-of-federal-university-gashua/
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-16. Retrieved 2022-05-17. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)