Jami'ar Tarayya, Gashua
Jami'ar Tarayya Gashua (Federal University Gashua) jami'a ce da ke jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya. [1][2]Cibiyar ilmantarwa da bincike ce mai neman warware bukatun al'umma na gaggawa tare da ba kowane mutum damar samun ilimi.
Jami'ar Tarayya, Gashua | |
---|---|
| |
Knowledge is Success | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Federal University Gashua |
Iri | jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Hedkwata | Gusau |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2013 |
fugashua.edu.ng |
Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan ne ya kafa jami'ar a shekarar 2013. Anyi hakan ne domin baiwa kowace jiha ta Najeriya (wadanda ba su da jami'ar tarayya) damar samun ilimi mai zurfi da baiwa dukkan jihohin damar samun ilimi daidai gwargwado.[3]
A cikin sake fasalin fannin ilimi da ci gabanta, gwamnatin tarayyar Najeriya a shekarar 2010, ta amince da kafa jami'o'i goma sha biyu (12) a shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida. Wannan ya kasance dan faɗaɗa damar samun ilimin manyan makarantu ga 'yan Najeriya. Domin tafiyar da jami’o’in yadda ya kamata, an kafa kwamitin aiwatarwa wanda ya hada da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFUND) da sauran masu ruwa da tsaki. Kwamitin ya yi shawarwari da gwamnonin jihohi na sabbin jami'o'in tare da duba wuraren da aka tsara kafin gabatar da rahotonsa a ranar 15 ga Nuwamba 2010. Aiwatar da rahoton kwamitin ya kasance cikin matakai. An fara aiwatar da kashi na farko tare da kafa Jami'o'i tara, a watan Fabrairun 2011. Aiwatar da kashi na biyu ya haɗa da kafa Jami'o'i uku ciki har da FUGashua a cikin Fabrairu 2013. A ranar 18 ga Fabrairu, 2013, an nada Farfesa Shehu Abdul Rahaman mataimakin shugaban jami’a, da Sulu Dauda, magatakarda (majagaba). A watan Yuni 2015, FUGashua ta ƙaddamar da ɗalibanta na majagaba 240. Shekaru uku bayan kammala karatun digiri na farko, yawan ɗalibai ya ƙaru sosai, kuma a cikin Fabrairun 2018, ɗalibai 990 ne suka kammala karatunsu.[4][5]
Ilimi
gyara sasheJami'ar Tarayya, Gashua tana ba da darussa sama da 20 a cikin tsangayoyinta (faculties) guda biyar.[6][7][8]
Tsangayar Ilimin Noma (Faculty of Agriculture)
gyara sashe- Tattalin Arzikin Noma da Fadadawa
- Ilimin Aikin Gina
- Ilimin Kimiyyar Dabbobi
- Ilimin Kifi da Kiwo
- Kula da Gandun Daji da Namun Daji
. Harkokin Tattalin Arziki na Gida da Gudanarwa / Tattalin Arziki
Tsangayar Ilimin Zaman takewa (Faculty of Humanity)
gyara sashe- Harshen Turanci
- Tarihi da Nazarin Duniya
- Karatun Musulunci
Tsangayar Ilimin Gudanarwa da Kimiyya (Management Science)
gyara sashe- Accounting
- Gudanar da Kasuwanci
ma'a
- Gudanar da Jama'a
Tsangayar Kimiyya (Faculty of Science)
gyara sashe- Biochemistry
- Halittu
- Chemistry
- Physics
- Lissafi
- Kimiyyan na'urar kwamfuta
- Kimiyyaar Siyasa
- IImin halin dan Adam
- Ilimin Zaman takewa
- Ilimin
min Zaman takewa
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2024-06-03. Retrieved 2022-10-13.
- ↑ https://www.campus.africa/university/federal-university-gashua-yobe-state/
- ↑ https://nigerianfinder.com/list-of-new-federal-universities-in-nigeria/
- ↑ https://www.pulse.ng/communities/student/federal-university-gashua-yobe-governor-excited-as-fugashua-gets-240-pioneer-students/qxxn3rt
- ↑ https://independent.ng/federal-university-gashua-matriculates-990-students/
- ↑ https://www.currentschoolnews.com/school-news/fugashua-courses-and-requirements/
- ↑ https://nigerianscholars.com/school-news/list-of-courses-offered-at-federal-university-gashua-fugashua/
- ↑ https://www.myschoolgist.com/ng/fugashua-courses/
- ↑ https://nigerianfinder.co