Mahdi Aliyu Gusau
Mahdi Aliyu Gusau Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Yana ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun mataimakan gwamnoni waɗanda suke da ƙarancin shekaru tun daga Jamhuriya ta huɗu a mulkin Najeriya. An haife shi a ranar 5 ga watan disamba a shekarar 1981, a garin Gusau, ya kuma yi karatu a kasar ingila inda ya karanta harkar Shari'a, Shi ɗa ne ga Janar Ali Gusau tsohon ministan tsaro.[1][2][3][4] a jamhuriya ta hudu (Fourth Nigerian Republic).
Mahdi Aliyu Gusau | |||
---|---|---|---|
2019 - 2023 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Gusau, 5 Disamba 1981 (42 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Lauya | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Tsigeshi daga mataimakin gwamna
gyara sasheA ranar Laraba 23 ga watan Fabrairu, a shekara ta 2022. Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau daga muƙaminsa, wanda ba tare da ɓata lokaci ba ta maye gurbin shi da Sanata Hassan Nasiha wanda ke wakiltar gundumar Gusau ta tsakiya.[5] Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da shugaban masu rinjaye, Faruku Dosara na APC daga Maradun ya gabatar a zauren majalisa a Gusau. Ƙudirin ya zo ne jim kaɗan bayan da majalisar ta amince da rahoton kwamitin mai shari’a Haladu Tanko, wanda ya binciki zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake zargin mataimakin gwamnan. Kakakin majalisar Hon Nasiru Muazu Magarya, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya umurci magatakarda, Saidu Anka, da ya gudanar da kaɗa ƙuri'a kan tsige mataimakin gwamnan Mahdi Aliyu daga muƙaminsa. Ƴan majalisa 20 daga cikin 22 da suka halarci taron sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsige mataimakin gwamnan.[6][7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "I won't appear before you, deputy governor tells Zamfara lawmakers" (in English). 2021-07-29. Retrieved 2022-02-22.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Akelicious (2019-05-29). "See The Youngest Deputy Governor In The History Of Nigeria". Akelicious (in English). Archived from the original on 2020-02-03. Retrieved 2020-02-03. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help)CS1 maint: unrecognized language (link) - ↑ "Zamfara Deputy Governor Mahdi Aliyu Gusau Archives". FRCN (in English). Retrieved 2022-02-23.CS1 maint: unrecognized language (link)[permanent dead link]
- ↑ Adesina, Michael (2019-09-25). "I'm qualified – Zamfara Dep. Gov clears air on his age". P.M. News (in English). Retrieved 23 February 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Sabi'u kad, Muhammad (23 February 2022). "(JUST IN): Zamfara Gets New Deputy Governor". tribuneonlineng.com. Retrieved 24 February 2022.
- ↑ George, Taiwo (23 February 2022). "Four Things To Know About The General's Son Impeached By Zamfara Assembly". dailytrust.com. Retrieved 23 February 2022.
- ↑ Olufemi, Ayodele (2021-07-29). "Zamfara Deputy Governor Impeached By State Assembly Lawmakers" (in Turanci). Retrieved 2022-02-23.