Ƙungiyar kwallon hannu ta mata ta Angola, wadda kuma ake yi wa lakabi da As Pérolas ( The Pearls ), ƙungiyar tana wakiltar Angola ne a gasar ƙwallon hannu ta ƙasa da ƙasa.
Angola ta shiga gasar Olympics har sau shida tun daga shekarar 1996, wato a 1996, 2000, 2004, 2008, 2012 da kuma 2016, inda ta zo ta 7 a shekarar 1996.
Angola ta halarci gasar cin kofin duniya sau 14 tun daga shekarar 1990, wato a shekarar 1990, 1993, 1995, 1997, 1999, 2001, 2003, 2005, 2007, 2009, 2011, 2011 . Yana da matsayi na 7 a cikin shekarar 2007 da matsayi Na 8 a cikin shekarar 2011 .