Karl Marx
Karl Marx shi ne marubuciya Jamus.
Karl Marx | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Karl Heinrich Marx |
Haihuwa | Trier (en) , 5 Mayu 1818 |
ƙasa | Kingdom of Prussia (en) |
Mazaunin | LandanTrier (en) |
ƙungiyar ƙabila | Ashkenazi Jews (en) Germans (en) |
Harshen uwa | Jamusanci |
Mutuwa | Landan, 14 ga Maris, 1883 |
Makwanci | Highgate Cemetery (en) |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (lung disease (en) ) |
Yan'uwa | |
Mahaifi | Heinrich Marx |
Mahaifiya | Henriette Presburg |
Abokiyar zama | Jenny von Westphalen (en) (19 ga Yuni, 1843 - 1881) |
Yara | view
|
Siblings | Emilie Conradi (en) , Louise Juta (en) , Mauritz David Marx (en) da Sophia Marx (en) |
Yan'uwa | view
|
Karatu | |
Makaranta | University of Jena (en) Gimnasium Real Frederick William III (en)(1830 -University of Bonn (en) (Oktoba 1835 - 1836) Humboldt University of Berlin (en)(Oktoba 1836 - : jurisprudence (en) , Falsafa |
Matakin karatu | Doctor of Philosophy (en) |
Thesis director | Bruno Bauer (en) |
Harsuna | Jamusanci |
Malamai | Friedrich Gottlieb Welcker (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai tattala arziki, ɗan jarida, historian (en) , mai falsafa, sociologist (en) , revolutionary (en) , maiwaƙe, ɗan siyasa da marubuci |
Wurin aiki | Köln |
Employers | Neue Rheinische Zeitung (en) Rheinische Zeitung (en) |
Muhimman ayyuka | Economic and Philosophic Manuscripts of 1844 (en)
Das Kapital (en) The German Ideology (en) The Communist Manifesto (en) |
Wanda ya ja hankalinsa | Georg Wilhelm Friedrich Hegel (en) , Max Stirner (en) , Ludwig Feuerbach (en) da The Essence of Christianity (en) |
Mamba | International Workingmen's Association (en) |
Suna | Glückskind |
Imani | |
Addini | mulhidanci |
Jam'iyar siyasa | Communist League (en) |
IMDb | nm0555631 |
Karl Marx masanin Falsafa ne Bajamushe, jigon jama'a, marubuci, masanin tattalin arziki, masanin tarihi. Bugu da kari, ya kasance mawaki, masanin harshe, dan jarida na siyasa kuma haziki masanin ilimin kimiya.
Cikakken sunansa Karl Heinrich Marx. An haife shi a ranar 5 ga Mayu, 1818 a cikin dangin Yahudawa a Trier (Prussia). A shekarar 1830 zuwa shekarar 1835. Ya yi karatu a Friedrich-Wilhelm Gymnasium. Sannan ya ci gaba da karatunsa a jami'o'in Bonn da Berlin, inda ya karanci shari'a, falsafa da tarihi.
Bayan kammala karatunsa a 1841, Karl ya sami digirinsa a fannin falsafa. Tare da matashiyar matarsa Jenny.Karl da Jenny sun san juna tin suna yara iyayen su abokai ne , ya ƙaura zuwa Bonn, yana da burin zama farfesa da koyarwa a jami'a. Amma ya zama edita kuma dan jarida na jaridar Rhine ta adawa, inda ya yi kakkausar suka ga gwamnati.
Jaridar Rhine Gazette ta kusan fito fili ta yi kira da a hambarar da daular Prussian tare da maye gurbinta da dimokradiyya. A shekara ta 1843, hukumomi suka rufe ofishin sa na edita,yayin da shida da matar sa suka koma Paris. A Paris Karl yana da abokai - masu ra'ayi irin nasa Friedrich Engels da Heinrich Heine.
Ba da daɗewa ba gwamnatin Faransa kuma kori ɗan jaridan ɗan tawaye (Karl) daga ƙasar saboda shiga cikin jaridar Vperyod mai tsattsauran ra'ayi. Karl ya tafi Brussels (Belgium) na tsawon shekaru uku, inda ya buga littafin Manifesto na Kwaminisanci, wanda suka rubuta tare da abokin sa Engels.
Daga nan sai Karl ya tafi Turai daga karshe ya koma Landan. A nan ya fara aikin jarida, amma sai ya ci gaba da aikin littattafai. A shekara ta 1859 aka buga littafinsa mai taken The Critique of Political Economy, kuma a shekara ta 1867 aka buga kundin farko na Capital.
Karl Marx a shekarar 1864 ya kafa ƙungiya a Landan ta ma'aikatan ƙasa da ƙasa na dukkan ƙasashe, daga baya ake kiranta da "First International". Wannan kungiya ta kasance har zuwa 1876.
Karl da Jenny sun haifi yara guda bakwai, amma hudu daga cikin su sun rasu tin suna yara . Ma'auratan sun rayu a tare har na tsawon shekara arba'in.Jenny ta mutu a 1881, haka zalika Karl Marx shima ya mutu bayan watanni biyu ta sanadiyyar matsala daya samu a huhun sa , yar farin Jenny ma ta mutu a janairun shekarar 1883.
Babban masanin falsafar Karl Marx ya mutu a matsayin marar kasa, mutumin da bashi da katin shedar kowace kasa. An binne shi kabari guda tare da matar sa , a makabartar Highgate dake Landan.