Justina Eze jami'in diflomasiyyar Najeriya ne kuma 'yar siyasa wacce ta kasance mamba a majalisar wakilai ta Uzo Uwani a lokacin jamhuriya ta biyu ta Najeriya. [1]

Justina Eze
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa Nsukka
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Nigerian People's Party (en) Fassara
Peoples Democratic Party
Justina Eze

Eze ta kasance tsohuwar jakadiyar Najeriya a Guinea Bissau da Cape Verde kuma tsohuwar jami'in hulɗa da shugaban ƙasa ga majalisar wakilai lokacin mulkin dimokuradiyya ta Olusgeun Obasanjo.[2]

Ita ce mace ta farko daga yankin Gabashin Najeriya da ta shiga majalisar wakilai a shekarar 1979.[3] Ta haɗa kai da Dr. Nnamdi Azikiwe da Cif Jim Nwobodo wajen gina jam’iyyar NPP, kuma tana ɗaya daga cikin mata uku da suka samu shiga majalisar wakilai ta tarayya a shekarar 1979. Tana kuma ɗaya daga cikin uwayen da suka kafa jam'iyyar People Democratic Party (Nigeria). Ta kasance tana karfafa mata da kuma shimfiɗa musu hanya a siyasa.

An haife ta ne a ƙaramar hukumar Nimbo/Uzuwani a shiyyar Sanata Nsukka ta jihar Enugu.

Manazarta

gyara sashe
  1. Shaibu, Inalegwu. "FUEL SUBSIDY: We can't afford to blow up Nigeria – Eze, first S/East female lawmaker". Vanguard.
  2. Uganwa, Austin (2014-11-22). Nigeria Fourth Republic National Assembly (in Turanci). Xlibris Corporation. ISBN 978-1-4990-8876-2.
  3. Africa Woman (in Turanci). Africa Journal Limited. 1980.