Junior Ajayi

Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya

Oluwafemi Junior Ajayi[1] (an haife shi ranar 29 ga watan Janairun shekara ta alif dari tara da casa'in da shida 1996), wanda aka fi sani da Junior Ajayi, kwararren Dan wasan kwallon kafa ne na Najeriya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a Kungiyar kwallon kafa ta Masarautar Smouha.[2][3]

Junior Ajayi
Rayuwa
Cikakken suna Oluwafemi Junior Ajayi
Haihuwa Lagos,, 29 ga Janairu, 1996 (28 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  CS Sfaxien (en) Fassara2015-20162810
Al Ahly SC (en) Fassara2016-202110330
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya2018-201810
Al-Nasser SC (en) Fassara2022-2022
Smouha SC (en) Fassara2022-64
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Ataka
Lamban wasa 27
Tsayi 185 cm

Najeriya ce ta zabe shi a cikin tawagar Yan wasa 18 da za su buga gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016,[4] bayan ya taimaka musu wajen neman tikitin zuwa Rio da manyan ƙwallayensa. Da Najeriya, ya lashe lambar tagulla ta Olympics. Junior Ajayi ya taimaka wa Kattai na Masar Al Ahly don tabbatar da Gasar Cin Kofin CAF 2, 2019-20 da 2020-21. Duk da haka, bayan zuwan Percy Tau da Luis Miquissone, Pitso Mosimane bai taba zaba shi don wasanni ba kuma ya bukaci Al Ahly ya dakatar da kwangilarsa. A karshe ya tsinci kansa a yankin Al Nasr-Benghazi na Libya. A rant 30 ga watan Yulin 2022, Junior Ajayi ya koma Masar ta hanyar sanya hannu a Smouha SC na Alexandria.

Aikin kulob

gyara sashe

CS Sfaxien

gyara sashe

Junior Ajayi ELFnan ya koma kulob din Sfaxien na Tunisiya a cikin watan Satumban 2015, ya halarci wasanni 28 a gasar ta Tunisiya da minti 2388, ya zura kwallaye 10 sannan ya zura kwallaye bakwai sannan aka hukunta shi sau biyu da katin gargadi, sanye da lamba 11 da Sfaxien na Tunisia. da adadinsu daya da tawagar Olympics ta Najeriya.[5][6]

Al Ahly SC

gyara sashe

Al Ahly a hukumance ya rattaba hannu kan kwantiragi da shi a lokacin canja wuri na bazara don zama dan wasa na biyu da ya shiga kungiyar ja daga CS Sfaxien bayan Ali Maâloul, kan dala miliyan $2,500,000, ya zura kwallaye hudu a wasanni goma.

Al Nasr-Benghazi

gyara sashe

Bayan kawo ƙarshen kwantiragin Junior Ajayi da Al Ahly Junior Ajayi ya zama dan wasa kyauta kuma ya rattaba hannu a Kungiyar Al Nasr Benghazi ta Libya a matsayin kyauta.

Smouha SC

gyara sashe

Kungiyar Smouha SC ta kasar Masar ta sayi Junior Ajayi kan kwantiragin shekaru 3, inda ya zama kulob na biyu na Masar da dan wasan na Najeriya ya taka leda.

Girmamawa

gyara sashe
  • Gasar Premier ta Masar : 2016–17, 2017–18, 2018–19, 2019–20
  • Kofin Masar : 2016–17, 2019–20
  • Gasar cin kofin Masar : 2017, 2018
  • CAF Champions League : 2019-20, 2020-21
  • CAF Super Cup : 2021
  • Lambar tagulla ta Olympic: 2016

Manazarta

gyara sashe
  1. https://digitalhub.fifa.com/m/fb00fb4f430e88fc/original/vfolbncwswkxqi8ostba-pdf.pdf
  2. http://www.filgoal.com/articles/270659/%D8%AE%D8%A8%D8%B1-%D9%81%D9%8A-%D8%A7%D9%84%D8%AC%D9%88%D9%84-%D8%B1%D8%B3%D9%85%D9%8A%D8%A7-%D8%A3%D8%AC%D8%A7%D9%8A-%D8%A3%D9%87%D9%84%D8%A7%D9%88%D9%8A
  3. https://mobile.btolat.com/video/31851
  4. https://www.espn.com/soccer/
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-29. Retrieved 2023-03-29.
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-29. Retrieved 2023-03-29.

Hanyoyin hadi na waje

gyara sashe