Jamila Nagudu
Jamila Umar Nagudu[1] (an haifeta a ranar 10 ga watan Agusta, a shekarata alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985). wacce aka fi sani da Jamila nagudu, ƴar wasan Kannywood ce ta Najeriya.[2][3]Jarumar ta yi fina -finai da dama irin su Indon ƙauye 2
Jamila Nagudu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 10 ga Augusta, 1985 (39 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo da jarumi |
Jamila da Jamilu
Tutar So
Matar Aure
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Jamila Nagudu a ranar 10 ga Agustan shekarar 1985 a cikin garin Magana Gumau, ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi, Najeriya . Jamila ta yi makarantun firamare da sakandare a jihar Bauchi.[ana buƙatar hujja]
Sana'a
gyara sasheJamila Umar wacce aka fi sani da Jamila Umar Nagudu ta fara fitowa a masana’antar Kannywood a shekara ta 2002. Tun lokacin da ta rabu, ta yanke shawarar fara fim. Ta bar Bauchi ta koma Kano ta gane cewa ta cimma burinta na zama jarumar fina-finai a masana'antar Kannywood. Ta kasance a harkar fim a matsayin mai rawa tun (a shekarar 2002). Sannan daga baya ta shiga harkar fim kaɗan kaɗan. Ƙoƙarin da ta yi a harkar nishadantarwa da wasan kwaikwayo ya jawo hankalin daraktoci har suka fara nuna ta a cikin fina-finansu. Jamila na iya fitowa a kowace rawa. Ta fito a fina-finan soyayya amma wani lokacin ma tana fitowa a fina-finan barkwanci. Nagudu ta yi fice sosai a Kannywood ta yadda ake yi mata lakabi da "Sarauniyar Kannywood". Darakta Aminu Saira shi ne ya fara jefa ta a fim din "Jamila da Jamilu" a matsayin jaruma.[4] An zaɓe ta a matsayin mafi kyawun Nollywood a Abeokuta.[5]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheJalima ta rabu da mijinta kuma tana da ɗa.[6][7] yaron ta a yanzu haka ya zama matashin saurayi, tayi aure da dama amma a yanzu haka bata da aure.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://kannywoodsceneblog.wordpress.com/tag/jamila-nagudu/
- ↑ "Tarihin Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)". Haskenews-All About Arewa. Retrieved 2022-03-25.
- ↑ Adeleye, Kunle (2021-12-25). "Meet The Queen Of Kannywood, Jamila Umar Nagudu: Full Biography". Glamsquad Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-03-25.
- ↑ "'Ibada da fim ne suka fi muhimmanci a wurina'". BBC News Hausa. 2018-04-04. Retrieved 2022-03-25.
- ↑ Online, Tribune (2017-09-16). "BON Awards: Jamila Nagudu, Omotola, others get nominations". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2022-07-28.
- ↑ "Ba ni da saurayi a Kannywood — Jamila Nagudu". BBC News Hausa. Retrieved 2022-03-25.
- ↑ "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-03-25.