Inuwa Wada
Muhammadu Inuwa Wada (c. 1917 – Nuwamba 25, 2015) dan majalisa ne kuma ministan ayyuka da jin ra'ayin mutane, ne, a karkashin mulkin gwamnatin Tafawa balewa.[1] Ya kasance gogaggen dan majalisa ne, a ƙarshen zangon jamhuriyar Najeriya ta farko, kuma an ba shi mukamin tsaro a shekarar 1965 bayan rasuwar Muhammadu Ribadu. An fara zaben shi a shekarar 1951 a matsayin dan majalisar dokokin Arewa, daga nan kuma aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya sannan ya zama mamba, kuma daga baya minista daga shekara ta 1951 zuwa 1966. Mutane da yawa sun san Inuwa Wada a matsayin mutum mai nutsuwa sabanin yawan bukatu da ministocin sa ke yi a sashen ayyuka da ke ci gaba da mayar da hankali kan manyan ayyukan raya kasa a wani shiri na shekaru shida a farkon shekarun 1960.
Inuwa Wada | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1917 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 25 Nuwamba, 2015 |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haife shi a shekara ta alif dari tara da sha bakwai (1917), ya fito daga dangi mai daraja a Kano, Dan uwa ne ga Malam Aminu Kano, Alhaji Aminu Bashir Wali kuma mahaifin tsohon shugaban kasa Murtala Mohammed, kakansa shi ne Cif Alkali a farkon karni na ashirin, kuma mahaifinsa ya yi aiki a matsayin Ma'aikacin surveyor na Hukumar Kano kafin rasuwarsa a shekarar 1924.
Wada ya halarci makarantar firamare ta Shuhuci kuma a shekarar 1938 ya kammala makarantar Middle ta Kano. Daga nan sai ya ci gaba da horar da malamai a babbar kwalejin Katsina daga 1933-1938 sannan ya zama malami a Kano inda ya koyar da; Tarihi da Turanci da ilimin nazarin ƙasa-(geography), sannan kuma ya yi aiki a matsayin edita a jaridar, ‘Yadda Yake Yau’. Bayan ya share shekaru tara yana koyarwa, sai ya bar wannan sana’a zuwa ofisoshin hukumar Yan asalin Kano, inda ya yi aiki a matsayin magatakarda da babban magatakarda da kuma jami’in yaɗa labarai.
Kasuwanci
gyara sasheInuwa Wada, ya samu lamuni daga bankin ci gaban masana’antu ta Najeriya don fara sana’ar sa ta farko ta masana’anta, kamfanin haɗa ashana. Daga baya ya koma wasu harkokin kasuwanci guda biyar ciki har da kamfanin sufuri. Wannan ci gaban da ya samu a fannin sufuri ya faru ne a lokacin da ya sayi manyan motoci 50 a kan kudi kadan, sauran kamfanoni sun haɗa da Nigerian Spanish Engineering Company, Kanol Paints, Arewa Industries, Standard Industrial Industries da Nigerian Enamelware Company.
Siyasa
gyara sasheWada ya fara siyasa ne a shekarar 1945 kuma ya kasance memba a jam'iyyar Arewa People's Congress. Yayin da yake jam'iyyar NPC, ya kasance sakataren jam'iyyar kuma mai tsara shirye-shirye-(na taruka ko wani abun) na jam'iyyar na kasa. A cikin shekarun 1950, ya yi aiki a hukumar gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Najeriya, Kamfanin Coal Corporation na Najeriya da Hukumar Tallan Groundnut ta Najeriya. A zaɓen 1964 sai da ya fafata da wani matashin ɗan takarar daga jam'iyyar NEPU wanda malamin makaranta ne mai suna Musa Said Abubakar Magami kuma gwamnan Kano na gaba Abubakar Rimi wanda ya tsaya takara mai zaman kansa amma duk sun janye daga takarar kafin a fafata zaɓen.[2] Wada kawu ne ga marigayi Murtala Mohammed, tsohon shugaban Najeriya. Ya gudanar da kasuwancin sufuri cikin nasara bayan juyin mulkin 1966 wanda ya soke jamhuriya ta farko. Ya kuma kasance mai tasiri a yankin Arewa bayan juyin mulkin.
Tarihin zabe
gyara sashe1959 Sumaila, Zaben dan majalisa Inuwa Wada NPC - 26,149 Mohammed Achimolo Garba NEPU - 2,231 Sule Baba AG - 456
Manazarta
gyara sashe- ↑ Vanguard (25 November 2015). "Hundreds of people attend funeral prayer for Inuwa Wada in Kano". Vanguard News. Vanguard. Retrieved 15 January 2016.
- ↑ Feinstein, Alan. The Life and Times of Nigeria's Aminu Kano. African Revolutionary. p. 204. ISBN 978-156-299-4.