Ifeoma Okoye
Ifeoma Okoye (an haifeta a shekarar 1937) a jihar Anambra dake yankin gabashin ƙasar. magoya bayanta sun kira ta "mafi mahimmancin marubuciyar mata daga Najeriya bayan Flora Nwapa da Buchi Emecheta ," a cewar Oyekan Owomoyela.
Ifeoma Okoye | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Anambra, 1937 (86/87 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Marubiyar yara da marubuci |
Employers |
Nnamdi Azikiwe University Aston University (en) |
Muhimman ayyuka | Behind the Clouds (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Ifeoma a shekarar 1937 a Jihar Anambra, Najeriya; (ba a san ainihin ranar da aka haife ta ba).
Karatu da Aiki
gyara sasheTa je makaranta a Kwalejin St. Monica da ke Ogbunike kuma ta sami takardar koyarwa. Sannan ta koyar a kwalejin St. Monica na tsawon shekaru biyu. A tsakanin shekarun 1963 zuwa 1967, ta halarci makarantar All Saints International School a Enugu. Ta gudanar da makarantar gandun daji a Enugu daga shekara ta, 1971 zuwa 1974. Daga shekara ta, 1974 zuwa 1977, Okoye ta tafi karatu a Jami'ar Najeriya, Nsukka, inda ta samu Digiri na farko a fannin Turanci. Daga shekara ta, 1986 zuwa 1987, ta yi karatu a Jami’ar Aston da ke Ingila, inda ta samu digirin digirgir a fannin Turanci. Daga baya, ta koyar da Turanci a Jami'ar Nnamdi Azikiwe har zuwa shekara ta, 2000.[1]
Ta tafi makaranta a Kwalejin St. Monica da ke Ogbunike don samun shaidar koyarwa a shekarar, 1959. Daga nan ta kammala karatu daga Jami'ar Najeriya da ke Nsukka don samun digirin digirgir a fannin Ingilishi a shekara ta, 1977. Ta rubuta litattafai ciki har da Bayan girgije, litattafan yara da gajerun labarai, kamar The Village Boy da Eme Goes School.
Littattafai
gyara sasheDuk da cewa an san Okoye da gajerun labarai na yaranta, amma kuma ta rubuta wasu littattafai na manya, kamar Behind the Clouds. Bayan girgije ya kasance game da ma'aurata da suka kasa haihuwar 'ya'ya, da kuma yadda laifin yafi yawa akan mace maimakon namiji.
Kyaututtuka
gyara sasheOkoye ta karɓi kyaututtuka na duka Bayan Bayan girgije da The Village Boy daga Majalisar Fasaha da Al'adu ta Najeriya a cikin 1983, tare da samun mafi kyawun almara na kyautar shekara don littafin labari Maza marasa kunne, a 1984.
Lambar yabo
gyara sasheA shekarar 1985, ta sake samun wata lambar yabo ta Daily Bread bayan Eze a wurin baje kolin littattafan Ife na kasa. Ta kuma kasance Gwarzon Yankin Afirka na Gasar Gajerun Labarai na Common wealth a shekarar, 1999.[2]