Hadiza Isma El-Rufai

Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Najeriya, marubuciya

Hadiza Isma'il El-Rufa'iAudio file "Ha-Hadiza Isma'El-Rufai.ogg" not found (An kuma haife ta ne a ranar ashirin da daya 21 ga watan Yuni, a shekara ta alif dari tara da sittin 1960) miladiya.(Ac)Yar Najeriya ce, kuma marubuciya, wacca itace uwargidan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Hadiza ce ta kafa cibiyar nan na Yasmin El-Rufai Foundation (YELF), cibiya dake maida hankali gurin koyar da ilimi ga mata da ƙananan yara, musamman rubutun ƙirƙira da nazari.

Hadiza Isma El-Rufai
Rayuwa
Haihuwa Kano, 21 ga Yuni, 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a Marubuci

Tarihi gyara sashe

An haifi Hadiza Isma El-Rufa'i a cikin birnin Kano, Najeriya, ga mahaifinta Mohammed Musa Isma tare da uwargidansa Amina Iya Isma.[1] Mahaifinta ma'aikacin gwamnati ne.

Hadiza tayi karatun ta na BSc da MSc a fannin gine-gine a shekara ta alif dari tara da tamanin da uku (1983) da kuma MBA a shekara ta alif (1992) duk daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, sannan ta sake yin Masters a Rubutun Kirkira (Creative Writing) a shekara ta 2012 daga Jami'ar Bath Spa, United Kingdom.[2]

Daga nan ne, tafara aiki a matsayin malamar jami'an, a sashen koyar da zane-zane (Architecture) a Kaduna Polytechnic, sannan tayi aiki a hukumar wutan lantarki ta ƙasa wato (National Electric Power Authority, NEPA), kafin nan tazama ma'aikaciya mai zaman kanta. El-Rufa'i najin harsuna uku Hausa, Turanci da Faransanci.

Rayuwar Iyali gyara sashe

A shekara ta alif Dari tara da tamanin da biyar (1985), ta auri Malam Nasir Ahmad El-Rufai wanda suka haɗu dashi a shekara ta alif dari tara da sabain da shida (1976 ) a makarantar share fage wato (School of Basic Studies), na Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.[3] Wanda daga baya yazama Ministan Babban Birnin Tarayya a Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Kaduna.

Aikin Rubuce-rubuce gyara sashe

A shekara ta ( 2017), Hadiza Isma El-Rufai ta wallafa littafinta ''An Abundance of Scorpions'' (Ouida Books).[4] littafin nobel ne, wanda tasamu ƙwarin-gwiwa daga aikin data taba yi na sakai a wani gidan marayu dake babban birni Abuja, da kuma Son ta na tayi rubutu akan maraya.[5] An gabatar da littafin a Aké Arts and Book Festival na shekarar (2017).[6]

Helon Habila ya bayyana aikin marubuciyar amatsayin, "wani labari mai ratsa zuciya akan rashi da kuma zaburarwa akan karfin mace da jajircewan ta" wato (a turanci "a heartbreaking tale of loss and an uplifting story of a woman's strength and determination").[7][8]

Taimako (Agaji) gyara sashe

Tare da mijinta, El-Rufai suka kafa Yasmin El-Rufai Foundation (YELF) a shekara ta (2013) domin tunawa da yar'su wacce ta rasu a gidan ta dake birnin London a watan Nuwanba na shekara ta ( 2011).[9][10] Cibiyar koyarwar an bude shine a shekara ta (2017)[11][12] da kudurin rainon yara akan kirkire-kirkire, "musamman ya'ya mata, tsakanin shekaru (8) zuwa(19)" da kuma mata masu tasowa, ta hanyar sama masu da "kayayyaki tare da malamai da littafai da zasu bukata dan karin fahimtar karatun su."[13][14]

A matsayin ta na Uwar-gidan Jihar Kaduna, ta cigaba da amfani da ofishinta wurin ayyukan jinƙai da taimakawa marasa karfi,(talakawa) ta bayar da magunguna ga masu ciwon amosanin jini wato sickle cell patients a garin Kaduna da kewaye.[15][16][17]https

Manazarta gyara sashe

  1. "Yasmin El-Rufai Foundation: Promoting literacy, creative writing". Blueprint – For Truth and Justice. November 11, 2017.
  2. "Board Member-HADIZA ISMA EL-RUFAI | Safari Books". safaribooks.com.ng. Archived from the original on 2017-10-14. Retrieved 2019-02-27.
  3. "I used to sing in the Catholic Church choir – Hadiza El-Rufai". Punch Newspapers.
  4. Bivan, Nathaniel (November 16, 2017). "Hadiza El-Rufai to present new book at Ake Festival". Daily Trust. Archived from the original on March 25, 2019. Retrieved February 27, 2019.
  5. "How orphans triggered my latest novel – Hadiza El-Rufai (DailyTrust) – Sabi News". sabinews.com. Archived from the original on 2019-09-14. Retrieved 2019-02-27.
  6. "Kaduna Gov's Wife, Hadiza El-Rufai urges Nigerians to adopt orphans – The Elites Nigeria". theelitesng.com.
  7. "Hadiza Isma El-Rufai". Ouida books. Archived from the original on 2019-01-22. Retrieved 2019-02-27.
  8. "First Lady of Kaduna, set to release her Debut Novel – An Abundance of Scorpions – The Afro Reader". The Afro Reader. October 18, 2017.
  9. "SERENDIPITY – Creative Writing, Yasmin and I (An Essay) by Hadiza Isma El-Rufai". Su'eddie in Life n' Literature. April 27, 2013.
  10. "I used to sing in the Catholic Church choir – Hadiza El-Rufai". Punch Newspapers.
  11. Aza, Msue (July 23, 2017). "Tears As el-Rufai, Aisha Buhari, Others Launch Yasmin El-Rufai Foundation". Leadership Newspaper. Archived from the original on March 6, 2019. Retrieved February 27, 2019.
  12. "Politics – El-Rufai Breaks Down in Tears Over Late Daughter". Nigerian Bulletin – Nigeria News Updates.
  13. "I used to sing in the Catholic Church choir – Hadiza El-Rufai". Punch Newspapers.
  14. "Yasmin El-Rufai Foundation: Promoting literacy, creative writing". Blueprint – For Truth and Justice. November 11, 2017.
  15. "Nigeria: Mrs. El-Rufai Donates Drugs to Sickle Cell Patients in Kaduna state Community Care Pharmacy»". June 7, 2017.
  16. "Mrs El-Rufai donates drugs to sickle cell centre".
  17. "Mrs. El-Rufai Donates Drugs to Sickle Cell Patients – Nigeria News by PRESS". press.com.ng. Archived from the original on 2019-03-25. Retrieved 2019-02-27.