Yasmin Foundation wata gidauniya ce da Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta samar domin taimakon ilimin yara da mata, kasancewar mata a arewacin Najeriya na fuskantar matsalolin rayuwa musamman wurin samun ingantaccen ilimi. Gidauniyar na bayar da dama ga mata dan samun horo akan ilimin ƙirƙira da rubuce rubuce, sannan da tallafawa marubuta samun ƙarin ilimi akan basirarsu ta hanyar basu gurbin karatu kyauta. Har wayau gidauniyar na gayyatan shahararrun marubuta a duk ƙarshen wata da suzo su bayar da labari akan hanyoyi ko cigaban da suka samu, dan ƙara ƙarfin gwiwa ga ƙanana masu tasowa.

Yasmin El-Rufai Foundation

Manazarta gyara sashe