Gona
Gona wani waje ne ko kuma wani fili ne mai faɗi da manoma suke keɓewa don aikace-aikacen noma. Kama daga noman tsirrai da kuma kiwon dabbobi da kiwon kifi, da dai sauransu. Ana amfani da kayayyakin aikin gona iri-iri kamar, fatanya, garma, Gatari Adda, sungumi da dai sauransu. Wani lokaci manoma ko kuma masu aikin gona suna fuskantar matsaloli, na rashin wadatattun kuɗin siyen kayayyakin aikin gona, Kamar: takin zamani da waɗansu abubuwan Noma. Haka kuma manoma suna fuskantar kalubale dangane da matsalar ambaliyar Ruwa,[1] itama tana kawo musu cikas, haka kuma fari shima yana karya manoma.
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
artificial geographic entity (en) ![]() ![]() |
Mamallaki | Manoma |
Amfani |
farming (en) ![]() |
NCI Thesaurus ID (en) ![]() | C48953 |