Sungumi
Sungumi ko kuma Sangwami yana daga cikin kayan aikin gona wanda ana amfani dashi ne wajen shuka amfanin gona.
Ya nada doguwar Ƙota dogon kotan shine ya banbance tsakanin shi da kwashe. Yadda ake Amfani da sungumi mutum biyu suke aiki da shi ɗaya na sara wajen da za'a zuba iri (ƙwayar shuka) ɗaya kuma na biye dashi yana sanya irin wajen sarin da akayi da sungumi, yanayi yana rufewa (turbuɗewa). Sai dai wasu yankunan basa amfani da sungumi sai dai Shantu da dai sauran abubuwan da ake yin shuka dasu, irin jihar Zamfara, Sokoto da kuma jihar Kebbi sune suka fi amfani da sungumi.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Sangwami". hausadictionary.com. Retrieved 28 December 2021.