Godfrey Chitalu, wanda ake yi wa laƙabi da Ucar (an haife shi a ranar 22 ga Oktobar 1947 -ya rasu a ranar 27 ga Afrilun 1993), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Zambiya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba . Ana dai kallonsa a matsayin ɗan wasan da ya fi kowanne ɗan wasan ƙasar Zambiya, kasancewar yana riƙe da tarihin zura kwallo a ragar tawagar ƙasar kuma an zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan ƙwallon Zambiya na bana har sau biyar.[1][2][3][4][5][6][7][8][9][10] A cikin shekarar 2006, CAF ta zaɓe shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun 'yan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka 200 a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Godfrey Chitalu
Rayuwa
Haihuwa Luanshya (en) Fassara, 22 Oktoba 1947
ƙasa Zambiya
Mutuwa Libreville, 27 ga Afirilu, 1993
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Kitwe United F.C. (en) Fassara1964-1970
  Ƙungiyar kwallon kafa ta kasar Zambiya1968-198010876
Kabwe Warriors F.C. (en) Fassara1971-1982
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Zambiya ta ce Chitalu ya ci ƙwallaye sama da 100 a dukkanin gasa a shekarar 1972, wanda ya zarce yawan ƙwallayen Gerd Müller a wannan shekarar da kuma jimillar Lionel Messi a shekarar 2012, biyun da ‘yan jarida ke kiransu da cewa. tarihin duniya". [11][12] An gabatar da binciken a cikin shekara ta 2012 bayan Lionel Messi ya karya rikodin zargin Gerd Müller na duniya. Duk da haka, mai magana da yawun FIFA ya bayyana cewa ba a taɓa samun tarihin hukumar ta FIFA ba saboda ba sa lura da wasannin cikin gida.

Bayan ya yi ritaya, Chitalu ya dauki aikin horas da 'yan wasan ƙasar Zambiya a lokacin da daukacin 'yan wasan suka halaka a wani hadarin jirgin sama a gabar tekun Gabon a ranar 27 ga Afrilun 1993.

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin sunayen manyan 'yan wasan kwallon kafa na maza na duniya da suka zira kwallaye a kasar
  • Jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa na maza masu buga wasan kasa da kasa 100 ko fiye
  • Jerin 'yan wasan kwallon kafa na maza masu kwallaye 50 ko fiye na kasa da kasa

Manazarta gyara sashe

  1. Zimba, Jack (31 January 2010). "Lest we forget them". The Post (Zambia). Archived from the original on 18 December 2012. Retrieved 27 December 2010.
  2. Muchimba, Jerry (24 May 2012). "Samuel "Zoom" Ndhlovu: True Zambian Legend". Bolazambia. Retrieved 9 July 2012.
  3. Maradas, Emmanuel. "Interview with Ndaye Mulamba Living Legend". Simbasports. Archived from the original on 7 September 2009. Retrieved 17 June 2009.
  4. "Dennis Liwewe talks to Fast Track". BBC. 9 May 2002. Retrieved 10 June 2009.
  5. Jerry Muchimba (9 November 2012). "Zambia National Team Appearance and Scoring Records". Zamfoot. Retrieved 23 November 2012.
  6. Chibulu, Musonda "Stars of yester-year – Solly Pandor: True Zambian Legend" Zambia Daily Mail, 14 August 2010 p.10
  7. "Profile: Before Lionel Messi, there was Godfrey Chitalu". The Score. 17 December 2012. Archived from the original on 19 December 2012. Retrieved 16 December 2012.
  8. Ekai, Claudia (13 December 2012). "Chitalu's record spins football world". Supersport. Retrieved 17 December 2012.
  9. Pilgrim, Sophie (17 December 2012). "Zambia's Chitalu 'scored more goals than Messi'". France24. Retrieved 17 December 2012.
  10. Guerrero, Jose (15 December 2012). "Kamanga: "El Derby County vino dos veces para fichar a Chitalu"". as.com. Retrieved 15 December 2012.
  11. "Super League History". Football Association of Zambia. Archived from the original on 13 January 2012.
  12. Cummings, Michael (11 December 2012). "Godfrey Chitalu: Did Zambian Striker Score More Goals Than Lionel Messi?". Bleacher Report. Retrieved 29 March 2013.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe