Bill Mallon

Likitan tiyatar kashi, ɗan wasan golf kuma masanin tarihi

William James Mallon (an haife shi ranar 2 ga watan Fabrairu, 1952) likitan tiyatar kashi-(Orthopedic surgery) ne na Amurka, kuma tsohon ƙwararren ɗan wasan golf kuma mai jagoran wasannin Olympics.

Bill Mallon
Rayuwa
Haihuwa Paterson (en) Fassara, 2 ga Faburairu, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Karatu
Makaranta Duke University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a orthopedic surgeon (en) Fassara, Masanin tarihi, golfer (en) Fassara, likitan fiɗa da orthopedian (en) Fassara
Kyaututtuka

Rayuwar farko da Fara Aiki

gyara sashe
 
Bill Mallon

An haifi Mallon a Paterson, New Jersey.[1] Ya yi karatu a Jami'ar Duke kuma ya kammala karatun (magna cum laude) da sakamakon A.B. a fannin lissafi da Ilimin Kimiyyar abubuwa (physics). Yayin da yake Duke ya buga wasan golf na kwaleji kuma ya kasance All-American sau biyu, haka-zalika sau biyu ya na zaɓar fitattun 'yan wasan Kwaleji na Amurka kuma ya kasance ɗan takara sau biyu a gasar NCAA. Ya lashe gasa sama da 40 na wasan masu tasowa (amateur) da suka haɗa da; ƙwara biyu kowanne a gasar Massachusetts Amateur da New England Amateur. [1] Har ila yau, ya lashe Middle Atlantic Amateur sau ɗaya. [1]

A matsayin ƙwararre

gyara sashe

A shekara ta 1975, Mallon ya zama ƙwararre. [1] Ya shiga PGA Tour bayan ya cancanci kammala Fall 1975 PGA Tour Qualifying Schooll.[1] Mallon ya buga wasanni tsawon kaka huɗu, daga 1976 zuwa 1979, an zabi mafi kayatarwa uku acikin 10 na wasanni da ya kammala.[2] Wasansa mafi kyayatarwa shi ne na 5 a 1977 Joe Garagiola-Tucson Open. Mallon ya taka leda a gasar 1977 U.S. Open, kuma ya kasance sau biyu a cikin mutane 100 a jerin masu kudin gasar.

Aikin likita

gyara sashe
 
Bill Mallon

Bayan barin PGA Tour, Mallon ya koma Jami'ar Duke don karantar karatun likitanci a matsayin M.D. a 1984. Ya zauna a cibiyar kula da lafiya ta Jami'ar Duke tsakanin 1984 zuwa 1990 kuma yanzu shine Mataimakin Farfesa na Orthopedics kuma yana da nasa aikin na kashin kai. Mallon ya ƙware a ɓangaren haɗa/gyaran ko tiyatar kafaɗa da tiyatar gwiwar hannu kuma shi mabiyin ƙungiyar Cibiyar Nazarin Orthopedic Surgeons na Amurka, ne Hakazalika , memba na Likitan Jiki na Amurka da Jikin gwiwar hannu, inda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban wurin a shekarar 2012, kuma zai zama shugaba wurin a 2014, kuma memba. na majalisar shawara na Cibiyar Kula da Magungunan Wasanni. Ya yi rubuce-rubuce sosai kan batun raunin wasanni kuma ya kasance editan likita na mujallar Golf Digest tun 1987. A baya Mallon ya kasance editan Arewacin Amurka na Jaridar Shoulder and Elbow Surgery.

Masanin tarihin Olympics

gyara sashe

Har ila yau Mallon shi ne babban jami'i a tarihin gasar Olympics kuma ya rubuta littattafai 24 kan wannan batu. Ya kasance abokin haɗin gwiwa kuma daga baya shugaban kungiyar masana tarihi na Olympics na kasa da kasa kuma ya kasance mai ba da shawara kan tarihi ga kwamitocin shirya wasannin Olympics na Atlanta da Sydney. Mallon ya kasance mai ba da shawara kan ƙididdiga ga kwamitin Olympics na kasa da kasa kuma an ba shi lambar yabo ta Olympics a azurfa a shekara ta 2001 saboda hidimar da ya yi ga Olympics.

Nasarori a matakin mai tasowa (amateur)

gyara sashe

Nasarori a matakin ƙwararre (professional)

gyara sashe

Select bibliography

gyara sashe
  • Quest for Gold. Leisure Press New York City 1984 08033994793.ABA (with Ian Buchanan)
  • The Olympic Record Book. Taylor & Francis. 1988. 08033994793.ABA.
  • Who's Who der Olympischen Spiele 1896–1992. Agon-Sportverlag Kassel 1992 08033994793.ABA (with Erich Kamper)
  • The Golf Doctor : How to Play a Better, Healthier Round of Golf. Macmillan. 1996. 08033994793.ABA (with Larry Dennis).
  • Historical Dictionary of the Olympic Movement. Scarecrow Press. 1996. 08033994793.ABA (with Ian Buchanan)
  • The 1896 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 1997. 08033994793.ABA (with Ture Widlund).
  • The 1900 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 1997. 08033994793.ABA.
  • The 1904 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 1999. 08033994793.ABA.
  • The 1906 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 1999. 08033994793.ABA.
  • The 1908 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 2000. 08033994793.ABA. (with Ian Buchanan)
  • The 1912 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 2001. 08033994793.ABA. (with Ture Widlund)
  • The 1920 Olympic Games: Results for All Competitors in All Events. With Commentary. McFarland & Company, Jefferson (North Carolina) 2003. 08033994793.ABA. (with Anthony Bijkerk)
  • Orthopaedics for the House Officer. Williams and Wilkins 2000 (with McNamara and Urbaniuk)
  • Ernest Amory Codman: The End Result of a Life in Medicine. WB Saunders 1999

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 PGA Tour. The PGA Tour Book 1978. p. 112.
  2. "Bill Mallon – Career Stats by Season". databaseGolf.com. Retrieved September 26, 2013.
  3. 3.0 3.1 "Past New England Amateur Champions" (PDF). Archived from the original (PDF) on April 26, 2012. Retrieved November 22, 2011.

Hanyoyin haɗi na Waje

gyara sashe