Gladys Anoma
Gladys Anoma (1930 - Oktoba 26, 2006) farfesa ce mai ilimin kimiyya kuma 'yar siyasa ce daga Ivory Coast a Yammacin Afirka.[1]
Gladys Anoma | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Gladys Rose Bonful | ||
Haihuwa | Grand-Bassam (en) , 28 ga Maris, 1930 | ||
ƙasa | Ivory Coast | ||
Mutuwa | 15th arrondissement of Paris (en) , 26 Oktoba 2006 | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Paris (en) | ||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwa
gyara sasheAnoma 'yar Joseph Anoma ce, kuma yayin da daga baya aka san ta da Gladys Anoma, an ba ta suna Bonful Gladys Rose Anoma lokacin haihuwar ta.[1] Ta kasance ɗaliba a Senegal na tsawon shekaru huɗu sannan a Faransa na tsawon shekaru biyu.[1] Ta sami digiri na uku a fannin tsirrai na wurare masu zafi[2] daga Sorbonne, a Paris, Faransa, sannan ta ziyarci Tunisiya, Jamus, Ingila, Habasha, Morocco da Ghana kafin ta kai shekaru 37.[3]
A cewar labarin ta, ta yi aure da HE Ambassador J. Georges Anoma. Kuma taana da ’yar’uwa mai suna Mrs. Aké.[3]
Rahoton wata jarida game da balaguron mako biyar da ta yi zuwa Kingston, New York a watan Agusta 1968, tare da wasu shugabannin mata 11 na Afirka, ta ce mijinta, a lokacin, shi ne Sakatare Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje kuma ma’auratan suna 'ya 'ya huɗu. Makasudin tafiyar shi ne don gano "al'amurra masu tada hankali a Amurka da Afirka."[3]
Ta rasu a birnin Paris a shekara ta 2006 kuma an binne ta a Abidjan na ƙasar Ivory Coast.[4] An gudanar da bikin tunawa da ita a cocin Saint Jacques Two Plateaux for Anoma a cikin shekarar 2016, shekaru 10 bayan mutuwarta.[3]
Nasarorin da ta samu
gyara sashe- Dr. Anoma ta koyar a Jami'ar Abidjan, Ivory Coast.[3]
- Ta kasance marubuciyar rubutun labarin kan flora na Ivory Coast wanda ya bayyana a cikin shekarar 1971.[5]
- A siyasance, tare da Jeanne Gervais da Hortense Aka-Anghui, ta kasance ɗaya daga cikin mata uku da aka zaɓa a Majalisar Dokokin Ƙasar Ivory Coast nan da nan bayan samun 'yancin kai; Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar shugaban kungiyar daga shekarun 1975 har zuwa 1989.[2]
- Ta kasance sakatare-janar na Association des Femmes Ivoriennes (Ƙungiyar Matan Ivory Coast) na shekaru masu yawa.[2]
Wallafawa
gyara sashe- Kammacher, Paul, Adjanohoun, Edouard, Assi, L Ake, Anoma, Gladys. LA FLORE AGROSTOLOGIQUE DE COTE D'IVOIRE . Ma'anar Botanischen Staatssammlung Munchen. 10, 1971, shafi na 30-37. H. Merxmüller. Munchen.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Mme Bonful Gladys Rose Anoma". www.necrologie.ci. Archived from the original on 2019-11-07. Retrieved 2020-05-04.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Kathleen E. Sheldon (2005). Historical Dictionary of Women in Sub-Saharan Africa. Scarecrow Press. ISBN 978-0-8108-5331-7.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 "The Kingston Daily Freeman from Kingston, New York on August 19, 1968 · Page 17". Retrieved 29 September 2017.
- ↑ "Cote d'Ivoire: ASCAD - To a great lady, the grateful Nation". fr.allafrica.com (in Faransanci). Retrieved 2020-05-04.
- ↑ 5.0 5.1 "Anoma, Gladys – Biodiversity Heritage Library". www.biodiversitylibrary.org. Retrieved 29 September 2017.