Ganiyu Abiodun Johnson ɗan siyasar Najeriya ne kuma tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Oshodi-Isolo II a jihar Legas. [1]

Ganiyu Johnson
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Oshodi/Isolo II
Rayuwa
Haihuwa Lagos Island, 17 ga Yuni, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Southern California (en) Fassara
Matakin karatu Digiri a kimiyya
master's degree (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

An fara zaɓen Johnson a matsayin ɗan majalisar wakilan Najeriya a shekarar 2019 don wakiltar mazaɓar tarayya ta Oshodi-Isolo II a jihar Legas amma a shekarar 2023 Jese Okey-Joe Onuakalusi na jam'iyyar Labour ya doke shi. [2]

Ya kasance kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Legas ga Gwamna Akinwunm Ambode a shekarar 2015 kafin ya yi murabus ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a shekarar 2019. [3] [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "My bill on 5 years practice for doctors will mitigate effects of brain drain — Rep. Johnson - Daily Trust". dailytrust.com/ (in Turanci). 2023-04-18. Retrieved 2024-12-10.
  2. Oyero, Kayode (2023-09-04). "Oshodi Constituency: Tribunal Upholds LP's Onuakalusi, Dismisses APC's Petition". Channels Television (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  3. "Ganiyu Abiodun Johnson's Endearing Feats – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2024-12-10.
  4. Ogundairo, Abiodun (2016-08-18). "Lagos Infrastructure: Govt commences fly-over at Pen Cinema Junction". GuardianTV (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.