Tsibirin Lagos

Karamar hukuma ce a jahar najeriya

Lagos Island,muhimmin wuri ne dake tsakiyar Karamar hukumar Lagos dake Jihar Lagos, Nijeriya. Tsibirin ya mamaye yammacin yankinsa, sannan ya kasance daya daga cikin yankunan Lagos. A kidaya da aka gudanar na 2006 ya sanya mutanen wurin a matsayin kimanin mutum .209,437 sannan tana da fadin 8.7 km2.

Tsibirin Lagos


Wuri
Map
 6°27′N 3°24′E / 6.45°N 3.4°E / 6.45; 3.4
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaLagos
Yawan mutane
Faɗi 209,437 (2006)
• Yawan mutane 978.68 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 214 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Lagos Lagoon
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 101223
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho +234

Bayanin wuri gyara sashe

Wurin na nan a kan tafkin Lagos, a daf da wani katafaren gabar teku dake kariyar daga Afurka, asalin tsibirin ya kasance gida kuma wurin kamun kifi,ga yarbawan Iko wanda ta habaka zuwa birni dake Lagos a yau. A yanzu tsibirin ya fadada har zuwa sauran tsibirai da kuma ainihin doron kasar garin Lagos.

Gadoji uku suka hada tsibirin da kuma ainihin doron kasar garin Lagos sune; Gadar Carter Bridge, da Eko Bridge da kuma Third Mainland Bridge wanda suka ratsa daga Tafkin Lagos zuwa gundumar Ebute Metta. Har wayau ta wadannan ake bi aje sauran tsibiran Victoria Island da kuma Ikoyi. Gabar teku na gundumar Apapa dake Lagos yana daura da tsibirin. Wurin ya samar da cibiyoyin kasuwanci na Lagos, sannan akwai manya manya gidajen gwamnati da shaguna da kuma ofisoshi a wajen.

A tarihance, Lagos Island ya kasance mazaunan mutanen Brazil ne a yayin da mafi akasarin bayi da suka dawo gida suke zama. Akwai mutane da yawa a unguwar Broad Street dake Marina.

Akwai yankin talakawa daga kudancin tsibirin inda ke da gidaje na talakawa. Akwai cunkosa matuka a tsibirin kuma anyi yunkuri da dama wajen inganta shi ta hanyar zuba tituna da zasu kara saukin hada-hada. A wannan yankin ne sarkin Lagos, Oba of Lagos ya zauna. An kuma yi amanna cewa a wannan yanki kadai za'a iya tsara al'adun gargajiya na Eyo (Eyo Festival) a Lagos.

Tattalin arziki gyara sashe

Mafi yawancin manya manyan ofisoshi na bankunan Najeriya na cikin Tsibirin kamar su First Bank, UBA dake da ofishi a Marina, da dai sauran su. Sannan akwai sauran ofisoshin bada hayan gidaje,da na wutan lantarki, manyan 'yan kasuwa da sauran su dake yankin Marina a cikin tsibirin.

Alamar kasa da wararen bude idanu gyara sashe

Tom Jones Memorial Hall And Library gyara sashe

Yana nan a unguwar Nnamdi Street, Idumota wanda aka fi sani da Victoria St, Tom Jones Memorial hall wuri ne da ake tunawa a mtasyin wajen da mutanen zikists suka taru don samar da mafita nagari a watan November, 1948. Amintattu daga mutane da Thomas Jones ya zaba suka gina wurin wanda ya rasu a 1913, daga cikin wasiyar sa shine a gina wuri na karatu (Library) a sanya sunansa.

Freedom Park gyara sashe

Freedom Park yana daya daga cikin manyan wuraren bude idanu yana nan a tsibirin Lagos Island. Wurin bude idanun ya kasance a da kurkuku ne, a can baya lokacin mulkin mallaka kuma ana kiransa da suna Her Majesty's Broad Street Prisons. An samar da wurin don tunawa da kuma kakanni da suka sha gwagwarmaya a lokacin turawan mulkin mallaka wajen neman 'yancin kasa. An bude wurin a shekara ta 2010 a yayin da Najeriya ta cika shekara 50 da samun 'yanci. Sannan akwai shirye-shirye da aka gudanar yayin bikin budewar, wanda suka hada da wasannin kwaikwayo, wakoki, drama da gabatarwa da dai sauransu. Sannan mutum zai iya shakatawa a tafkuna da sauran wuraren shakatawa da ke wajen....Cite error: Invalid <ref> tag; refs with no name must have content