Femi Falana

Lauyan Najeriya ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam

Femi Falana, SAN (an haife shi ranar 20 ga watan Mayu,a shekara ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da takwas (1958) Miladiyya.[1][2]

Femi Falana
Rayuwa
Haihuwa jahar Lagos da Ilawe Ekiti (en) Fassara, 20 Mayu 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Funmi Falana
Yara
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam, Lauya da Babban Lauyan Najeriya
Kyaututtuka
falanafalana.com.ng

lauyan Najeriya ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin dan adam.[3][4] Shi ne mahaifin mawakin rapper Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz. Falana sanannen mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama ne, a ko da yaushe yana ƙoƙarin nuna tausayi ga mutane.[5] Ya shahara wajen adawa da zalunci, daga hukumomin soja da suka biyo baya.[6]

 
Femi Falana

Femi Falana[7] ɗalibi ne a makarantar St. Michael daga 1963 zuwa 1968. Bayan kammala wannan makaranta, Femi Falana ya halarci Makarantar Katolika ta Sacred Heart daga 1971 - 1975, ya fara aikin shari'a a shekarar 1982. Bayan kammala aikin lauya a 2012, Femi Falana ya zama babban lauya a Najeriya, inda ya kammala karatunsa a Jami'ar Ife a yanzu da aka sani da; Jami'ar Obafemi Awolowo Ile Ife Osun. Babban abokin tarayya ne a Falana&Falana Chambers wanda yake gudanarwa tare da Funmi Falana matarsa. Ya tsaya takara amman ya sha kaye a zaɓen gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar National Conscience Party, jam’iyyar da ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa a shekarar 2011.[8]

Shi ne mahaifin Falz, fitaccen mawakiyan Najeriya, mawakin mai wasan barkwanci kuma ƴar wasan kwaikwayo,[9] wadda matarsa mai fafutukar kare hakkin mata ce a Najeriya, Funmi Falana.[10] Yana cikin ƙungiyoyin ƙwararru da yawa: Ƙungiyar lauyoyin Afirka ta Yamma, Memba, Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya kuma memba, Ƙungiyar Lauyoyin Afirka ta Yamma, Memba, Ƙungiyar Lauyoyin Afrika ta Pan African da Memba, Ƙungiyar Lauyoyin Duniya.[11][12][13]

Ya rubuta wallafe-wallafe da dama da suka haɗa da "Siyasar Mulki a Post Military Nigeria Fundamental Rights Enforcement, Legaltext Publishing Company 2005.

Manazarta

gyara sashe
  1. Abeni, Margaret (2017-06-28). "The FAMOUS FIGHTER for human rights in Nigeria! Who is he?". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2021-10-10.
  2. Admin. "MR. Femi Falana, HLR". Hallmark of Labour. Archived from the original on 25 January 2019. Retrieved 24 January 2019.
  3. "Femi Falana". informationng.com. Retrieved 1 December 2015.
  4. "Femi Falana". okay.ng. Retrieved 6 August 2018.
  5. Abeni, Margaret (2017-06-28). "The FAMOUS FIGHTER for human rights in Nigeria! Who is he?". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2021-10-10.
  6. Abeni, Margaret (2017-06-28). "The FAMOUS FIGHTER for human rights in Nigeria! Who is he?". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2021-10-10.
  7. Abeni, Margaret (2017-06-28). "The FAMOUS FIGHTER for human rights in Nigeria! Who is he?". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2021-10-10.
  8. "Femi Falana". nigerianbiography.com. Retrieved December 1, 2015.
  9. "My wife didn't like our son's music career –Femi Falana". The Punch. Archived from the original on August 24, 2015. Retrieved December 1, 2015.
  10. Simeon Ndaji (5 August 2012). "Femi Falana left me at the mercy of judges – Funmi,wife". Vanguard News. Retrieved 21 June 2016.
  11. Legalnaija (2017-08-18). "Star Profile – Mr. Femi Falana SAN, LL.B, B.L, FCI, Arb. - Legal Naija" (in Turanci). Retrieved 2021-06-01.
  12. Ifeoma, Peters. "Legal Luminary Profile: Femi Falana SAN - DNL Legal and Style" (in Turanci). Archived from the original on 2022-05-18. Retrieved 2021-06-01.
  13. "Femi Falana". Archived from the original on 2021-09-25.