Fashewar bututun Mai na Abule Egba, 2006

Fashewar bututun Mai a Legas, Najeriya da ya haddasa mutuwar ɗaruruwan mutane

Fashewar bututun mai na Abule Egba a shekara ta 2006 dai wani bala'i ne da ya abku a unguwar Abule Egba mai yawan jama'a da ke cikin birnin Lagos, Najeriya, a ranar 26 ga watan Disamba, 2006, inda fashewar ta kashe ɗaruruwan mutane. Da farko an yi imanin cewa an kashe mutane kusan 500, amma daga baya an tabbatar da cewa asarar bata kai hakan ba.

Fashewar bututun Mai na Abule Egba, 2006
explosion (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata 2006
Taswirar da ke nuna (wanda aka zagaya da jajayen) wurin Lagos, Nigeria.

Lamarin ya faru ne bayan da barayi suka huda wani bututun mai, mai ɗauke da man fetur[1] da tsakar dare (agogon Najeriya), lamarin da ya jawo hankalin daruruwan masu fasa bututun a gundumar da suka tattara man ta hanyar amfani da kwantena na robobi, ana zarginsu da zuba mai a cikin wata tankar mai, [1] kafin man ya fara zuba ƙasa ya kama da wuta.[2] Har yanzu dai ba a san musabbabin fashewar ba, yayin da shaidu suka bayyana cewa an fasa bututun ne lokacin da fashewar ta afku.[2]

Ba a fayyace adadin mutanen da aka suka rasa rayukansu, amma an tabbatar da cewa sun kai ɗari. Abiodun Orebiyi, babban sakataren kungiyar agaji ta kasa NRC, ya kiyasta cewa aƙalla mutane 200 ne suka mutu, amma ya nuna cewa babu adadin waɗanda suka mutu a hukumance, kuma ya kasa tantance adadin waɗanda suka mutu, yana mai cewa NRC “[ bai sani ba idan 300, 400 ko 500 ne".[2][3] Ya kuma ƙara da cewa an kai mutane 60 asibiti da munanan kone-kone,[3] yayin da aka lalata gidaje da dama, tare da wani masallaci da coci da ke kusa da wurin. [4] Wani babban jami’i mai suna Ige Oladimeji, an ruwaito yana cewa an samu rahoton mutuwar mutane 260 da dare.[5] A ranar da fashewar ta auku, wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kiyasta gawarwaki 500 a wurin.[4]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Zhang, Linda (29 December 2006). "Nigerian Pipeline Blast Spurs UN Call for Fuel Management Review". International Business Times. Retrieved 1 January 2007.
  2. 2.0 2.1 2.2 "200 dead in Nigeria pipeline blast, Red Cross confirms". CNN, originally Associated Press. 26 December 2006. Archived from the original on 2 January 2007. Retrieved 26 December 2006.
  3. 3.0 3.1 "Up to 500 killed in Lagos fuel blast". Reuters. 26 December 2006. Archived from the original on 16 February 2007. Retrieved 29 December 2006.
  4. 4.0 4.1 "Lagos pipeline blast kills scores". BBC News. 26 December 2006. Retrieved 26 December 2006.
  5. "Hundreds Die in Nigeria Pipeline Blast". Sky News. 26 December 2006. Retrieved 29 December 2006.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe