Fashewar bututun Mai na Atlas Creek, 2006
Fashewar bututun mai na Atlas Creek wani bala'i ne da ya afku a ranar 12 ga watan Mayun 2006 a tsibirin Atlas Creek (wani lokaci ana kiransa Isanki Island), kusa da Lagos, Nigeria, lokacin da ɓarayi suka fasa wani bututun mai da ya haifar da fashewar, hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane 150.[1] Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya ta ce tun da farko ɓarayin sun yi ramuka a cikin bututun don satar mai, daga nan ne mutanen yankin suka sauko da jarkoki domin cika su da Mai.[1] Kimanin jarkoki ɗari biyar ne aka gano a wurin da fashewar ta afku, wanda ya kona duk wanda ke da nisan tazarar mita 20 daga inda abin ya faru.[2] An binne mutane da dama da suka mutu a kusa da wani babban kabari.[3]
Fashewar bututun Mai na Atlas Creek, 2006 | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Kwanan wata | 2006 |
Bincike
gyara sasheShugaban kasa a lokacin, Olusegun Obasanjo, ya ba da umarni ga yan sanda don aiwatar da cikakken bincike akai.[3][ana buƙatar hujja]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Scores die in Nigeria fuel blast". BBC.co.uk. 12 May 2006.
- ↑ "Nigeria pipeline blast kills 200". Times of Malta (in Turanci). Retrieved 2022-08-26.
- ↑ 3.0 3.1 "Probe ordered after Nigeria blast". BBC.co.uk. 13 May 2006.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Scores die in Nigeria fuel blast Scores die in Nigeria fuel blast. Retrieved: 25 September 2011.
- Probe ordered after Nigeria blast Retrieved: 25 September 2011.