Evelyn Ndali Oputu (An haife ta ranar 13 ga watan Agusta, na shekarar 1949) ma'aikaciyar banki ce ta Nijeriya, kuma tsohuwar manajan daraktar Bankin Masana'antu.[1]

Evelyn Oputu
Rayuwa
Haihuwa jahar Delta, 13 ga Augusta, 1948 (76 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta St Teresa’s College Oke Ado (en) Fassara
Jami'ar Lagos
Makarantar Kasuwanci ta Harvard.
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Ma'aikacin banki

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Evelyn_Oputu ta fara karatun ta ne a kwalejin St. Teresa, Ibadan a shekarar 1960 sannan daga nan ta zarce zuwa Makarantar Fasaha da Kimiyya ta Tarayya da ke jihar Legas don samun takardar shedar kammala sakandare tsakanin shekarar 1965 da shekara ta 1967. Ta sami digirin B.Sc. digiri a kan harkokin kasuwanci daga Jami'ar Legas tsakanin shekarar 1972 da 1975 kuma daga baya ta sami difloma a Mass General Management a jami'ar Harvard Business School, Boston a shekarar 1987.[2]

Evelyn _Oputu Ta fara aikin banki a shekara ta 1976 tare da ICON Merchant Bank Ltd. sannan daga baya ta shiga Bankin Kasuwanci na Duniya (IMB) a shekara ta 1982 inda ta yi aiki ta hanyar Baitul Malin da Bankin Kudi na Babban Kasuwar, da kuma sassan ayyukan bada shawarwari na Project da Financial. Kuma a shekarar 1991, ta zama Babban Darakta, First Bank of Nigeria Plc tsakanin shekarar 1991 da zuwa shekara ta 1997 sannan daga baya ta yi aiki a matsayin Babban Darakta, Manajan Darakta na Bankin Masana'antu daga watan Disamba shekarar 2005 zuwa watan Afrilu shekara ta 2014.

Kyaututtukan da ta samu

gyara sashe
  • Order of Nigeria by the Nigeria Government
  • Banker of the Year 2013 by The Sun Newspapers
  • Leadership Chief Executive Officer (CEO) of the year 2012 by The Leadership Newspapers

Manazartai

gyara sashe
  1. "EVELYN NDALI OPUTU: – OUR INFLUENCER – YOUTHSNG" (in Turanci). Retrieved 2020-03-09.[permanent dead link]
  2. publisher. "Birthday [Evelyn Oputu]". Realnews Magazine (in Turanci). Retrieved 2020-03-09.