Evan Enwerem (29 Oktoba 1935 - 2 August 2007) dan siyasan Najeriya ne wanda ya yi Shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya a 1999. Ya kasance memba na Jam’iyyar Democratic Party ta Jama’a.

Evan Enwerem
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

3 ga Yuni, 1999 - 18 Nuwamba, 1999
Ameh Ebute - Chuba Wilberforce Okadigbo
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

1999 - 2003 - Amah Iwuagwu (en) Fassara
District: Imo East
Gwamnan jahar imo

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Anthony E. Oguguo (mul) Fassara - James N.J. Aneke (mul) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Ikeduru, 29 Oktoba 1935
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tarihin Mutanen Ibo
Harshen uwa Harshen, Ibo
Mutuwa Abuja, 2 ga Augusta, 2007
Karatu
Makaranta University of Southampton (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All People's Party
Peoples Democratic Party
tamabarin majalisar dattawa
hoton gidan wakilan dattawa na Nigeria

Farkon Rayuwa

gyara sashe

An haifi Evan Enwerem a Ikeduru, jihar Imo, Najeriya, a ranar 29 ga Oktoba 1935. Ya sami digiri na farko a Jami'ar Southampton da ke Ingila.

Enwerem ya kasance cikin rashin lafiya kafin rasuwarsa a 2007. Ya jima yana jinya a Asibitin kasa da ke Abuja, Najeriya na wani lokaci. A cewar rahotanni, iyalan Enwerem sun yi kokarin yin shirye-shiryen canza shi zuwa wani asibiti a kasar Jamus don jinya. Asibitin kasa da farko ya ki amincewa da bukatar dangin nasa, saboda rashin lafiyar Enwerem. Enwerem ya mutu da safiyar washegari 2 ga watan Agusta 2007, a Asibitin Kasa da ke Abuja yana da shekara 73. Ya bar matarsa Vivienne, da yara bakwai. Daya daga cikin yaransa, Mista Evan Enwerem jnr, an nada shi a matsayin Shugaban Kwamitin Rikon Ruwa na karamar hukumar Ikeduru.

http://allafrica.com/stories/200708030231.html https://www.iol.co.za/news/africa/nigerian-senate-president-impeached-20118