Donald Etiebet
Cif Donald Dick Etiebet (1934 - 21 Yuli 2015) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance sanata a jamhuriya ta biyu a Najeriya (1979 - 1983). Daga nan ne aka zabe shi gwamnan jihar Cross river tare da goyon bayan shugaban majalisar dattawa na lokacin Joseph Wayas da kuma Sanata Joseph Oqua Ansa duk sun kasance yan adawa da gwamna mai ci a lokacin Clement Isong, Fidelis Ikogo Nnang shi ne mataimakinsa, yana rike da wannan ofishin daga Oktoba zuwa Disamba 1983, lokacin da juyin mulkin soja ya kawo Janar [[Muhammadu Buhari ]kan karagar mulki.
Donald Etiebet | |||||
---|---|---|---|---|---|
Oktoba 1983 - Disamba 1983 ← Clement Nyong Isong - Dan Archibong →
| |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Donald Dick Etiebet | ||||
Haihuwa | Ikot Ekpene, 1934 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Mutuwa | 21 ga Yuli, 2015 | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Ibibio Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Nigeria Peoples Party |
Rayuwar farko da Aiki
gyara sasheAn haifi Etiebet a Ikot Ekpene a Jihar Akwa Ibom, Dan kabilar Annang. Ya auri Nike Maryam Agunbiade, daga Jihar Oyo a shekarar 1991, kuma suna da ‘ya’ya uku.[1] Kanensa Donatus ("Don") Obot Etiebet ya rike mukamin Ministan Makamashi a majalisar ministocin Ernest Shonekan na kankanin lokaci, inda ya ci gaba da rike mukamin bayan wancan, gwamnatin daJanar Sani Abacha ya tsigeshi, kuma daga baya ya zama dan takarar PDP na gwamnan jihar Akwa Ibom a shekarar 2007. [2]
Siyasa
gyara sasheBayan komawar dimokradiyya a 1999, Etiebet ya kasance shugaban jam'iyyar United Nigeria People's Party (UNPP), wacce daga baya ta hade da All People's Party (APP) wadda takoma jam'iyyar All Nigeria People's Party . (ANPP)An nada Etiebet Amatsayin mataimakin shugaban jam’iyyar ANPP ta Kudu. Daga baya Etiebet ya zama shugaban jam'iyyar ANPP na kasa bakidaya. Da yake magana da yawun jam’iyyar ANPP a watan Maris na shekarar 2003, Etiebet ya ce kamata ya yi a fitar da sakamakon zabe a rumfunan zabe kuma wakilan jam’iyyun siyasa su sanya hannu a kai a matsayin hanyar dakile tashe-tashen hankula a lokacin zabe. [3]
Shugaban majalisar koli
gyara sasheA matsayinsa na shugaban majalisar koli ta dattawa a jihar Akwa Ibom, a watan Maris na shekarar 2004, Etiebet ya jagoranci tawagar shugabanni daga jihar Akwa Ibom domin ganawa da shugaba Olusegun Obasanjo, inda suka tattauna kan dokar kawar da tsarin bakin teku wadda take raba kudaden shigar man fetur.[4]
Mutuwa
gyara sasheMista Etiebet,ya mutu ranar 21 ga watan Yuli, 2015, an yi jana’izar shi a gidan iyalansa da ke Oruk Anam, a karamar hukumar Oruk Anam ta jihar akwa ibom.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-12. Retrieved 2022-08-09.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/195032-ex-gov-donald-etiebet-buried.html
- ↑ http://medbox.iiab.me/kiwix/wikipedia_yo_all_maxi_2019-04/A/Donald_Etiebet
- ↑ https://thewhistler.ng/tag/donald-etiebet/